Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar dawowar makarantu na firamare da na sakandare domin cigaba da Karatu a sabon zangon na shekarar 2025/2026.
Wata sanarwa da daraktan wayar da kai na ma’aikatar Ilimi,ta Kano Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar ta bayyana cewa, daliban makarantu na kwana za su koma a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, yayin da daliban makarantu na rana za su koma a Litinin, 8 ga Satumba, 2025.
An shawarci iyaye da masu kula da yara su kula da wannan jadawalin domin tabbatar da cikakken bin doka, inda aka gargadi dalibai da ɗalibai mata da suka saba dokar cewa za su fuskanci hukunci.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, ya yi fatan alheri ga malamai da ɗalibai wajen sabon zangon karatu mai zuwa.
TST Hausa ta rawaito cewa wannan na nufin gwamnatin Kano tayi watsi da jita jitar karin lokacin komawa makarantu a Kano.
An gano yadda wasu ke yaɗa cewa za’a koma makarantun ne a ranakun 21 da 22 ga watan Satumba maimakon ranar 8 ga wata.

