Tsohon hadimin tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin yaɗa labarai wato Hon.Shehu Isa Direba ya yi kira ga mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shettima, da ya yi taka-tsantsan da shugaban hukumar kula da harkokin aikin Hajji ta kasa NAHCON Farfesa Abdullahi Sale Pakistan.
A cewar Shehu Isah Direba daga ranar da aka baiwa Pakistan wannan matsayi na Shugabancin NAHCON ya daina hulɗa da duk wanda ya taba taimaka masa a rayuwa.
Ya ce a gaban idonsa, Pakistan ya yi ikirarin cewa bai samu matsayin da yake kai ba ne saboda taimakon Ganduje ko kungiyar Izala ba ta kasa a samun mukaminsa.
A dan haka yace zaiyi sharafinsa ba tare da ya taimakesu ba ko ya dauki shawararsu.
Yace ya godewa Allah da ba Ganduje ne da Kungiyar Izala ne sukayi silar kawo shi ba.
Shehu Direba yace da Farfesa Pakistan yana daukar shawarar wadanda suka taimakeshi Kuma bai gujesu ba,da ba’a samu badakalar naira miliyan dubu 50 ,wanda hakan ya janyo ya bata sunan Kano da malaman Addini.
Ya nemi Kashim Shettima da yayi takatsantsan da Farfesa Pakistan wanda hukumar NAHCON ke karkashin kulawarsa.
A ranar 19 ga watan Augusta na shekarar 2024 ne Farfesa Pakistan ya kai ziyara ga Dr Abdullahi Umar Ganduje a Abuja kwana biyu bayan Shugaban kasa Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban hukumar ta NAHCON domin godewa Ganduje.
Tsohon mashawarcin na Ganduje ya gargadi duk wanda zai yi goyon bayan Pakistan da ya sani cewa zai fuskanci kalaman da ba su dace ba daga bakinsa kodai na butulci ko kuma na son zuciya.
Tsohon hadimin na Ganduje yace a madadin wasu daga cikin makusantan Dr. Abdullahi Umar Ganduje su na kira ga shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da shugaban NAHCON Farfesa Pakistan.
A baya bayan nan TST Hausa ta rawaito cewa, tsohon hadimin na Ganduje ya roki Shugaban kasa Bola Tinubu ko kuma Mataimakinsa Kashim Shettima da su dakatar da Farfesa Abdullahi Sale Pakistan daga Shugabancin NAHCON sakamakon zargin batan naira miliyan dubu 50 dake ake zargin wani dan uwansa ya karkatar daga hukumar.

