Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ranar Juma’a, 5 ga Satumba, 2025, za ta kasance hutu ga ma’aikatan Najeriya domin bikin Mauludi na ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar cikin gida, Dakta Magdalene Ajani, ya fitar a madadin Ministan ma’aikatar.
Sanarwar ta taya musulmi a Najeriya da kasashen duniya murna, tare da kira da su yi koyi da halayen Annabi na zaman lafiya,da ƙauna,da tawali’u, haƙuri da jin ƙai.
Haka kuma, sanarwar ta bukaci ‘yan Najeriya daga addinai daban-daban da su yi amfani da wannan dama wajen roƙon Allah ya kawo zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da goyon bayan ƙoƙarin gwamnati na haɗin kai da cigaba.
TST Hausa ta rawaito cewa Ministan cikin gidan ya yi fatan musulmi za su gudanar da bikin Maulud cikin farin ciki da lumana.

