Gwamnatin jihar Kano ta shirya taron bada horo na yini daya ga direbobin da suke tuka jiragen ruwa na kwale kwale a kananan hukumomi 19 na jihar..
An shirya taron ne domin magance yawan hadarin jiragen ruwa da ake samu a wasu yankuna na jihar Kano.
A yayinda yake kaddamar da fara taron karawa juna sanin a dakin taro na ma’aikatar, Sufuri ta jihar Kano mai rikon mukamin kwamishinan Sufuri Dr Adamu Aliyu Kibiya yace Gwamna Yusuf ne ya bada umarnin shirya taron ga direbobin kwale kwale a kananan hukumomi 19.
Yace wannan ne karo na farko kuma za’a cigaba da shirya taron lokaci zuwa lokaci.
Dr. Kibiya ya hori direbobin kwale kwalen da suyi amfani da Ilimin da suka samu wajen nuna ƙwarewa a yayinda suke aikin tuka kwale kwale a yankunansu.
TST Hausa ta rawaito cewa an rabawa mahalarta taron rigunan shiga ruwa ,kuma ana sa ran za’a rika rabawa duka fasinjojin da zasu rika hawa jirgin na kwale kwale.
Kananan hukumomin da direbobin suka fito sun hada da: Bagwai,Bebeji,Bichi,Bunkure,Gabasawa,Garko,Kabo ,Garun Malam,Ghari, Karaye,Madobi, Rano,Rimin Gado, Makoda,Minjibir,Rogo,Sumaila da kuma Tudun Wada.
A ranar 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2021 ne wani jirgin Kwale kwale ya kife da daliban Islamiyyya sama da 47 a garin Bagwai Inda sama da dalibai 25 suka mutu.
Haka zalika a ranar 21 ga watan Augusta na shekarar 2024 wani jirgin na kwale-kwale da ya ɗauko mutane sama da 10 ya gamu da hatsari a kauyen Kauran Mata da ke karamar hukumar Madobi.
TST Hausa ta rawaito cewa a wanann hadarin mutane huɗu ne daga cikin 10 suka mutu, kana an ceto wasu mutane biyar a lokacin.

