Kwamitin Wayar da Kai kan Rijistar Katin Zabe ya gudanar da ganawa da Shugaban Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano, a wani bangare na yunkurin fadakar da jama’a kan muhimmancin mallakar Katin Zabe na Dindindin (PVC).
Yayin ganawar, Shugaban Kwamitin kuma Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada cewa katin zabe shi ne babban makamin da ‘yan kasa za su yi amfani da shi wajen gudanar da hakkinsu na dimokuradiyya. Ya ce, ba tare da katin zabe ba, masu cancanta ba za su samu damar bayyana ra’ayinsu a zaben da ke tafe ba.
A nasa jawabin, Kwamishinan Kananan Hukumomi, Hon. Muhammad Usman Tajudeen, ya yaba wa kwamitin bisa wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatinsa. Ya kuma yi alkawarin hada kai da shugabannin al’umma, sarakunan gargajiya da kungiyoyin matasa domin tabbatar da cewa kowane dan kasa mai cancanta a yankin ya yi rijista kuma ya mallaki katin zabensa.
Kwamitin Wayar da Kai kan Rijistar Katin Zabe zai ci gaba da fadakarwa a dukkan kananan hukumomi don karfafa halartar jama’a a harkokin dimokuradiyya.

