Shugaban kamfanin SAGAMA HOMES and SAGAMA Construction Engineering Ltd, Alhaji Ali Nuhu, ya kai ziyara ta musamman gidan marayun jihar Kano, inda ya gabatar da tallafin kayan abinci domin tallafa wa marayu da masu kula da su.
A cikin kayan tallafin akwai shinkafa, taliya, man girki da sauran muhimman kayan masarufi da za su taimaka wajen rage wa gidan marayun ɗan nauyi a rayuwa, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar kayan abinci a kasuwanni.
Alhaji Ali Nuhu, ya bayyana cewa wannan ziyara da tallafi wani ɓangare ne na shirin kamfanin SAGAMA na bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma, tare da nuna kulawa ga waɗanda suka fi bukata a cikin al’umma.
Inda Yace “Kula da marayu da marasa galihu hakki ne da ya rataya a wuyanmu a matsayin mu na al’umma.
Wannan tallafi ƙaramin abu ne idan aka kwatanta da irin jajircewar da ake buƙata wajen tallafawa waɗannan yara,” in ji shi.
Masu kula da gidan marayun sun nuna matuƙar farin ciki da wannan ziyara, inda suka gode wa shugaban kamfanin bisa irin wannan hidima da kulawa, tare da yi masa addu’ar samun nasara a dukkan harkokinsa.
Wannan aiki na alheri ya sake tabbatar da cewa kamfanin SAGAMA ba wai kawai ya tsaya kan gine-gine da ayyukan raya kasa ba, har ma yana ɗaukar nauyin zamantakewar al’umma wajen tallafawa gajiyayyu da marayu.

