Rahotanni sun tabbatar da mutuwar tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na Najeriya, Solomon Ehigiator Arase, wanda ya mutu a yau Lahadi, 31 ga Agusta, 2025, a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja.
An haifi Arase a ranar 21 ga Yuni, 1956 a karamar hukumar Owan West ta jihar Edo.
Ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya kammala digiri a fannin siyasa a shekarar 1980, kafin ya shiga aikin dan sanda a watan Disambar 1981.
Daga baya, ya samu digiri na lauya daga Jami’ar Benin da kuma digiri na biyu daga Jami’ar Lagos.
Arase ya yi aiki a wurare daban-daban ciki har da Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Akwa Ibom, da Babban Kwamandan Sashen Leken Asiri, da kuma Shugaban sashen binciken kwakwaf na manyan laifuka wato Criminal Intelligence and Investigation Bureau (CID).
Haka kuma, ya wakilci Najeriya a aikin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Namibia, sannan ya kasance Fellow a Nigerian Defence Academy (NDA).
Solomon Arase ya zama Sufeto Janar na yan sandan Najeriya na 18 daga watan Afrilu 2015 zuwa watan Yuni 2016,a zamanin mulkin Shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari kafin ya yi ritaya.
A shekarar 2023, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), amma daga bisani Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga wannan mukami a shekarar 2024.
TST Hausa ta rawaito cewa har yanzu ba a fitar da cikakken jawabi daga iyalansa ko rundunar ‘yan sanda kan mutuwar tasa ba.

