Tsohon mashawarcin tsohon Gwamnan Kano, Dr.Abdullahi Umar Ganduje, kan harkokin yada labarai, kuma jigo a jam’iyar APC reshen Kano Hon. Shehu Isah Driver, ya yi kira ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da ya gaggauta dakatar da shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale Pakistan, domin tabbatar da gaskiya a cikin bincike da ake yi kan hukumar.
Shehu Isah Driver ya bayyana cewa akwai zargi mai nauyi da ke nuna cewa kanin shugaban hukumar na da hannu a cikin wata badakalar kudi da ta kai naira biliyan hamsin (₦50bn) a hukumar.
A cewarsa, matakin dakatar da shugaban hukumar zai taimaka wajen baiwa hukumomin bincike damar gudanar da aikinsu cikin ’yanci da gaskiya ba tare da tsangwama ba.
Ya kuma jaddada cewa, gwamnati a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmad Tinubu na da alhakin tabbatar da cewa an gudanar da dukkan harkokin ibada, musamman aikin Hajji, cikin sahihanci da gaskiya domin amfanin al’ummar Najeriya.
Shehu Driver ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da su goyi bayan wannan bukata, domin tabbatar da adalci da kuma kare amana da kudaden al’umma.
TST Hausa ta rawaito cewa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta fara bincike mai zurfi kan Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) bayan rahotannin da suka nuna an yi amfani da naira biliyan 50 ba bisa ƙa’ida ba a lokacin gudanar da aikin Hajjin bana (2025).

