Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon dan majalisar dattawa daga Kano ta Kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya jinjinawa Jagoran jam’iyar NNPP na Najeriya Sanata Rabiu Musa kwankwaso abisa kishin da ya nuna na yan Arewa da aka rushe musu kasuwa ta Alaba Rago a Jihar Lagos.
TST Hausa ta rawaito cewa a farkon makon nan tsohon gwamnan jihar ta Kano Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara jihar ta Lagos Inda ya gana da masu ruwa da tsaki daga jihar da kuma shugabanin kasuwar ta Alaba Rago da aka rushewa wuraren kasuwancinsu.
A yayin ziyarar,Sanata Kwankwaso yayi Allah wadarai da matakin rushe kasuwar ta Alaba Rago.
Wannan tasa a wani sakon murya da daga daga cikin hadiman Sanata Kabiru Ibrahim Gaya wato Husaini Ambo Indbawa da ya gana da tsohon dan majalisar kuma ya aikewa da TST Hausa yace dole a yabawa Kwankwaso abisa kishin jama’arsa da ya nuna a Lagos.
Kabiru Gaya yace maganar neman hakkin yan Arewa da suke kasuwanci a Lagos ba magana ce ta siyasa ba ,kuma ya zama wajibi Shugabannin Arewa suyi koyi da Kwankwaso wajen nuna kishin mutanansa.
Tsohon sanatan ya kuma shaida cewa zai nemi Kwankwaso domin jin halin da mutanan kasuwar ta Alaba Rago ke cikin bayan rushe musu wajen Sana’arsu.
Ya tabbatar dacewa daga cikin tuntubar da zaiyiwa Kwankwaso harna neman a gudanar da taro na musamman domin kwatowa Yan Arewa hakkinsu.
Kabiru Gaya yace babu shakka dole a Kalli Kwankwaso a matsayin jagora a Arewa saboda kishin jama’arsa.
Yace kasuwar Alaba Rago ta shafe sama da shekaru 50 da yan Arewa suka kafata,amma rana daya a tashesu.
A Juma’ar nan ,itama Kungiyar dattawan Arewa da ta tuntuba sunyi Allah wadarai da matakin da gwamnatin Lagos ta yi na rushe kasuwar.

