Daga daga cikin mahaifiyar yan mata ukun da sukayi nasara a gasar Turanci ta duniya da aka gudanar a Ingila Hajiya Fatima Muhammad Mairiga yace kuɗin da aka baiwa yaransu, ministan ilimi na kasa ne ya bayar a aljihunsa ba daga asusun gwamnatin tarayya ba.
Hajiya Fatima Muhammad wacce itace mahaifiyar Rukayya Muhammad Fema tana wannan batu ne bayan cece kuce yayi yawa a kafafen sada zumunta kan kyautar naira dubu dari biyu da ake cewa gwamnanatin Tinubu ta baiwa Nafisa Abdullahi da tayi nasara a gasar Turanci ta duniya.
Fatima tace ministan ne da kansa yayi Wannan kyauta domin karrama daliban guda uku.
A wani faifen bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani wanda TST Hausa ta yi nazari akansa ,anga yadda Fatima Muhammad Mairiga ke cewa bayan ministan ya baiwa Nafisa Abdullahi naira 200,000 ya kuma baiwa Rukayya Muhammad Fema da Khadija Ibrahim Kalli naira 100,000 ko waccensu.
“Maraina kadan barawo ne ,wannan ce kallamar da ta fito daga bakin Fatima Muhammad Mairiga mahaifiyar Rukayya Muhammad Fema”
Saidai fa duk da haka an shiga cece-kuce a Arewa musamman a shafukan sada zumunta na zamani bayan da gwamnatin tarayya ta baiwa, Nafisa Abdullahi, kyautar kuɗin naira 200,000 a matsayin karramawa bisa nasarar da ta samu a gasar ƙasashen duniya na Ingilishi koda kuwa ministan ne ya bayar wasu na ganin abin kunya ne.
Wasu na ganin kuɗin ko minitan ne ya bayar sunyi kadan idan aka kwatanta da rawar da ta taka wajen wakiltar Najeriya a idon duniya.
A cewar su, bai dace a takaita irin wannan babbar nasara a kan naira dubu ɗari biyu ba, alhali gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawan gaske a wasu fannoni.
Sai dai wasu kuma sun bayyana cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne karramawar kanta, ba lallai sai adadin kuɗin ba.
A ganinsu, wannan alama ce ta yabo da kuma girmamawa daga gwamnatin tarayya ga jarumar, kuma hakan na iya ƙarfafa sauran matasa su yi ƙoƙari a fannoni daban-daban.
Masu sharhi sun ce wannan cece-kuce na nuna yadda jama’a ke da bambancin fahimta a kan yadda gwamnati ke karrama ‘yan Najeriya da suka yi fice a fagen ilimi, wasa ko al’adu.
A halin yanzu, tattaunawar na ci gaba da ƙara zafi a shafukan sada zumunta, inda jama’a ke bayyana ra’ayoyinsu kan darajar kyautar da kuma tasirin ta ga ci gaban matasan Arewa.

