Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa kira da take yi ga jama’a su mallaki katin zabe a shirye-shiryen zaben 2027, ba shi da wata alaka da siyasar kowace jam’iyya.
Gwamnatin tace kiran yana da alaka da cigaban jihar Kano da al’ummar ta baki daya da kuma makomarta a zaben 2027,Inda gwamnatin tace kiran ba na NNPP ko APC da PDP ba ne .
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya shine ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki da suka hada da yan gwagwarmaya da kungiyoyin fararen hula a cigaba da wayar da kan jama’a mahimmacin mallakar katin zabe da kwamatin da aka kafa yake cigaba da yi.
Kwamishinan ya ce manufar wannan kira ita ce tabbatar da cewa ‘yan kasa sun yi amfani da hakkinsu na dimokuradiyya ta hanyar kada kuri’a, ba wai goyon bayan jam’iyya ko dan takara ba.
Ya kara da cewa katin zabe na da muhimmanci wajen tabbatar da ingantacciyar dimokuradiyya, saboda haka gwamnati na kira ga dukkan mazauna jihar su yi rijista su karbi katin zabe domin kada su rasa damar zaben shugabanni da suka cancanta a 2027.
Kwamared Wayya wanda shine Shugaban kwamatin wayar da kan jama’a mahimmacin mallakar katin zaben da gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar ya nuna takaicinsa kan yadda ake neman mayar da Kano bayan wajen mallakar katin zaben.
Yace Kano wacce ita ce jiha mafi yawa amma ana neman barinta a baya ,idan aka kwatanta da jihohin kudancin Najeriya da suka dauki mallakar katin zaben da mahimmaci.
Kwamishinan yace har yanzu wadanda sukayi rijistar mallakar katin zabe ,ba su wuce mutane dubu 10 ba, yayinda wasu jihohin a Kudu suke da mutane dubu 300,wasu dubu 500 wasu ma sama da haka.
TST Hausa ta rawaito cewa taron kwamatin wanda shine karo na biyu ,ya hada da yan gwagwarmaya masu magana a kafafen yada labarai,da jagororin masu bukata ta musamman da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwamared Hassan Ibrahim Gama ya tabbatar da cewa za suyi aiki tare da kwamatin domin samun abinda ake bukata.
Ya nemi yan gwagwarmayar da su hada kansu domin samun nasara.

