Gwamnatin Kano ta nemi Mawallafa da suyi amfani da fasaharsu wajen shirya wakokin da za suja hankalin jama’a mahimmacin mallakar katin zabe.
Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ne ya bukaci hakan Inda ya yi kira ga mawaka da sauran masu rubuta wakoki da su mayar da hankali wajen shirya wakokin da za su wayar da kan jama’a kan muhimmancin mallakar katin zaben kafin zaben shekarar 2027.
Waiya wanda ya kasance Shugaban kwamatin wayar da kan jama’a mahimmacin mallakar katin zaben da gwamna Yusuf ya kaddamar, ya bayyana bukatar hakan ne a wajen taro na musamman da aka shirya tare da Mawallafan a ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano.
Kwamishinan ya ce katin zabe shi ne makamin ɗan ƙasa wajen zaben shugabanni nagari, don haka wajibi ne a ci gaba da tunatar da al’umma muhimmancin fitowa su karɓi katin su domin kada su rasa damar kada kuri’a a zabukan da ke tafe.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnati tana fatan za a samu haɗin guiwa tsakanin mawallafa da hukumomin yaɗa labarai domin isar da saƙon ga kowane yanki na jihar cikin sauƙi da kuma ingantacciyar hanya.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki , da dalibai, da mawaka karkashin jagorancin mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin Mawallafa Hon Tijjani Gandu inda suka bayyana shirinsu na rubuta wakoki da za su yi tasiri wajen jan hankalin jama’a kan mallakar katin zabe.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar Asabar data gabata ne kwamatin ya kai ziyara hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen Kano domin kulla alakar aiki da kuma karɓar shawarwari

