MAI RUBUTU:Dr. Nuraddeen Danjuma, na Jami’ar Bayero, Kano.
A halin da ake ciki na rashin tabbas da kuma sakacin gwamnati wajen kula da jami’o’in Najeriya, masana harkar Ilimi sun ce ya zama dole kungiyoyin ma’aikatan jami’a su hade,kansu domin rashin hadin kai na amfanar da gwamnati da marasa kishin Ilimi a Najeriya.
Kungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantu ta Najeriya (SSANU) a makon jiya ta zargi gwamnatin tarayya da fifita Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU).
Masana sun bayyana cewa wannan koke gaskiya ne, amma adreshin da aka kai shi ba daidai ba ne.
A cewar su, matsalar ba ASUU bace, matsalar ita ce dabarar gwamnati ta raba su da danniya.
A hakikanin gaskiya, duk kungiyoyin jami’a irinsu SSANU,da NASU, da NAAT da ASUU suna fama da matsaloli iri daya da suka hada da karancin albashi, da kin biyan hakkokinsu na baya, da tsofaffin kayayyakin aiki da ake fama da su a jami’oin Najeriya da kuma rashin kudaden gudanarwa.
Sai dai duk lokacin da gwamnati ta kira kungiyar daya domin tattaunawa, sauran kan tsaya gefe suna nuna kishi maimakon su mara wa juna baya.
Mai rubutun ya bayyana cewa duk da sukar da akeyiwa ASUU, ita ce ta dade kan gaba wajen kare martabar jami’o’in gwamnati da kuma neman walwalar malamai da sauran ma’aikata.
Mai sharhin ya nuna cewa duk wata nasara da aka samu ta hanyar gwagwarmayar ASUU, sauran kungiyoyi ma suna amfana da ita.
Sun kara da cewa lokaci ya yi da SSANU da sauran kungiyoyin jami’a su daina kallon ASUU a matsayin abokiyar gaba..
A cewar mai rubutun , abokin gaba shi ne sakacin gwamnati wajen bai wa ilimin jami’a muhimmanci, ba ASUU ba.
Idan har gwamnati na tattaunawa da ASUU kan albashi a kadaice, masana sun ce abin da ya dace shi ne sauran kungiyoyin ma su bukaci a hada su cikin tattaunawar, ba wai su tsaya a gefe suna kukan wariya ba.
Idan dukkan kungiyoyi suka hade da murya daya, za su fi karfi wajen matsa lamba ga gwamnati,” inji wani mai sharhi.
Akwai karin magana dake cewa idan kana son tafiya da sauri, ka tafi kai kadai; idan kana son zuwa nesa, ku tafi tare.
Masana harkar Ilimi sun yi kira da a yi tunanin domin a tafi yajin aikin kasa gaba daya wanda zai hada ASUU, SSANU, NASU da NAAT, ba domin muradun kansu kadai ba, sai domin neman gyara tsarin albashi da kuma inganta harkokin jami’oin gaba daya.
Mai rubutun ya yi nuni da maganar Nelson Mandela da yace mutukar aka samu hadin kai a ko menene za’a samu,nasara.
Masana sun kammala da cewa lokaci ya yi da ya kamata a samar da wani tsarin tabbatar da cimma bukatun ma’aikatan Jami’o’i a Najeriya da murya daya.
Sunce duk Inda aka samu rabuwar kai to akwai matsala.
Amma idan aka hade waje daya, zai Yi wuya a zalunci na kasa.

