Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai na zamani kan zargin karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-mali karya ne kuma shiri na siyasa da nufin bata suna.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar 22 ga watan Agusta, 2025, jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani labari da ya alakanta babban daraktan ofishin kula da al’amuran baƙi na fadar gwamnatin Kano, Alhaji Abdullahi Ibrahim Rogo, da almundahana.
Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace duk da cewa al’amarin yana gaban kotu a halin yanzu, gwamnati ta ga dacewar fayyace yadda ofishin kula da al’amuran baƙi ke aiki tare da jaddada matsayin ta kan gaskiya, rikon amana, da gaskiya a harkokin kudi.
1. Ayyukan Ofishin Kula da Al’amuran Baƙi
Duk wata fitar kuɗi zuwa ma’aikatu ko hukumomi ana yin sa ne bisa kasafin kudi tare da lambar musamman da aka ware. Babu wani jami’i da ke iya sarrafa kuɗin jama’a ba bisa ka’ida ba.
Ofishin kula da al’amuran baƙi na fadar gwamnati yana da alhakin shirye-shirye da suka shafi sufuri, masauki, walwala da tafiyar gwamnan a cikin gida da waje.
Haka kuma, yana daukar nauyin masauki da hidimar baƙi na musamman irin su shugabannin kasa, ministoci, jakadu, da sauran baki na musamman.
Saboda irin wannan aiki, fiye da kashi 95 cikin 100 na alhakin ofishin yana da nasaba da mu’amalar kuɗi, amma duk yana gudana ne bisa doka da amincewar gwamnati.
2. Matsayin Gwamnati
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana tsayin daka kan adalci, gaskiya, rikon amana da kin yarda da cin hanci da rashawa.
Gwamnati tana da cikakken kwarin gwiwa kan gaskiya da amincin babban daraktan, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo.
Gwamnati na maraba da suka na gaskiya da shawarwari na doka, amma ba zata lamunci sharrin siyasa ko yada labaran karya ba.
3. Rawar da Adawa ke Takawa
Gwamnati na sane da kokarin wasu daga cikin ‘yan adawa na amfani da kafafen zamani wajen yaudara da karkatar da hankalin jama’a.
A fili yake cewa gwamnatin da ta gabata ta karkatar da fiye da Naira biliyan 20 ta hannun ofishin kula da baƙi tsakanin watan Fabrairu zuwa Mayu 2023 bayan faduwar APC a zabe.
Jama’ar Kano ba su manta da bidiyon dala, barnar kwace filaye da dukiyar jama’a, da cin hanci da rashawa da suka yi katutu a shekaru takwas na mulkin APC ba.
4. Alkawarin Gwamnati ga Jama’a
A cikin shekaru biyu kacal, gwamnatin NNPP ta dawo da kwarin gwiwa, ta kuma jawo hankalin masu saka jari daga cikin gida da waje.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance daya daga cikin gwamnoni mafi samun lambar yabo a tarihin Jamhuriyar Hudu, wanda ke nuna gaskiya da shugabanci mai maida hankali kan jama’a.
Gwamnati na daraja kafafen yada labarai a matsayin abokan hulɗa wajen ilmantar da jama’a, tana kuma kira ga jaridu su tsaya kan gaskiya su guji zama kayan aiki ga ‘yan siyasa marasa kishin kasa.
5. Kammalawa
Gwamnatin Kano na sake jaddada cewa ofishin kula da al’amuran baƙi aiki ne na gudanarwa kawai, ba shi da ‘yancin kashe kudi da kansa. Duk wata mu’amala da yake yi ana yin ta ne cikin tsarin doka da kasafin kudi.
Zarge-zargen da ake yadawa ƙirƙira ne kawai domin karkatar da hankali daga shirye-shiryen gwamnati kafin zaben 2027.
Dukkan jami’an gwamnati, ciki har da babban daraktan, suna shirye a kowane lokaci su bayar da bayani ga hukumomin yaki da rashawa. Sai dai gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin doka akan wadanda ke yada sharri da nufin tunzura jama’a da zarge-zargen karya.
Ana kira ga jama’ar Kano da su yi watsi da wannan shiri na bata suna su ci gaba da goyon bayan gwamnati wajen ci gaba da samun shugabanci nagari, kare dukiyar jama’a, da inganta rayuwar al’umma.

