Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin shirya bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya shine ya jagoranci kaddamar da kwamatin,a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a ofishinsa.
Kwamared Wayya yace gwamnatin ta kafa kwamitin ne da nufin tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin nasara da kuma nuna rawar da jihar ke takawa a dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa.
Ya ce kwamitin zai tsara abubuwan da za a gudanar a fadin jihar, ciki har da ad’uoi da jawabai daga masana da wasanni, da kuma nune-nunen al’adu domin tunawa da irin gwagwarmayar da ta kai Najeriya ga samun ‘yanci a shekarar 1960.
A yayinda yake jawabi kwamishinan yaɗa labarai yayi kira ga al’umma da su ba da gudummawa da goyon baya domin ganin bikin ya gudana cikin kwanciyar hankali da haɗin kai.
A Jawabinsa na karbar Shugabancin kwamatin,mai rikon mukamin babban sakatare a ma’aikatar yaɗa labarai ta Jihar Kano, Alhaji Inuwa Idiris Yakasai ya yi alkwarin aiki tare da dukannin yan kwamatin domin samun abinda ake bukata.
Yakasai yace zasu tuntubi kowanne bangare na masu ruwa da tsaki a ciki da wajen kano dan gani basu baiwa gwamnatin Kano kunya ba.
TST Hausa ta rawaito cewa kwamatin ya hada da dukkanin bangaren hukumomin tsaro na Kano da suka hada da yan sanda da sojoji da hukumar shige da fice ta kasa reshen Kano da hukumar hana fasa kwauri wato kwastam da hukumar civil defense da hukumar kula da gidajen gyaran hali da hukumar Hisba da sauransu.
A ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2025 , Najeriya ke cika shekaru 65 da samun yancin gashin kai daga Turawa mulkin na Ingila

