Rahotanni nacewa an naɗa Alhaji Umar Faruk Muktar Maidattako a matsayin Chiroman Yola, lamarin da ya jawo hankalin jama’a daga sassa daban-daban na Najeriya da kasashen waje.
A wajen taron, Madakin Kano, Alhaji Yusuf Ibrahim Cigari, wanda ya jagoranci bikin, ya yi kira ga al’umma da su kasance masu da’a da biyayya ga shugabanni tare da yawaita dogaro ga Allah a duk lokacin da suka fuskanci kalubale na rayuwa.
Ya kuma shawarci sabon Chiroman da ya kasance jakada nagari a duk inda ya tsinci kansa, tare da kiyaye martabar gidansu, ta Yolawa da kuma masarautar Kano baki ɗaya.
A nasa jawabin, sabon Chiroman na Yola, Alhaji Umar Faruk Muktar Maidattako, ya gode wa Madakin Kano bisa ga wannan karamci da ganin dacewar nada shi, tare da yin alkawarin cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen kare mutuncin al’ummar Yola da jihar Kano a duk inda yake.
Bikin ya samu halartar dimbin jama’a daga cikin gida da wajen ƙasar.

