Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karbi bakuncin gwani Sanusi Bukhari Idris wanda ya zamo na uku a gasar Musabukar Karatun Al’qurani ta duniya da aka kammala a Kasar Saudiyya.
A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya fitar yace gwamna Yusuf ya taya matashin dan asalin jihar Kano murnar samun matsayi na uku a rukunin Qirā’āt da tafsiri a gasar Qur’ani ta ƙasashen duniya da aka gudanar a masarautar Saudiyya.
Wannan gagarumar nasara ba wai kawai alfahari ce gareshi da iyalansa ba, har ma abin farin ciki ne ga jihar Kano,da Najeriya baki ɗaya da kuma al’ummar musulmi gaba ɗaya acewar gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir, Inji Sanarwar.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa wannan nasara ta sake ɗaukaka sunan jihar Kano da ƙasar Najeriya a idon duniya, tare da tabbatar da irin kyakkyawan tarihi da jihar ke da shi wajen ilimin Qur’ani.
A ƙarshe, gwamnatin ta yi addu’ar Allah ya ci gaba da bashi Ilimi mai amfani ya kare shi, Ya kuma ɗaukaka matsayin sa wajen hidima ga addinin Musulunci da ɗan rayuwar al’ummar Kano musamman matasa.
Gwamnan a yayin karbar matashin gwani Bukhari ya yaba masa tare da bukatarsa ya cigaba da neman Ilimi.
TST Hausa ta rawaito cewa a watan Dismanbar shekarar 2024 ne , matashin Gwani Hafiz Sanusi ya yi nasara zama gwarzon shekara a Musabukar da akayi ta Najeriya karo na 39 a jihar Kebbi.
Bayan kammala Musabukar ne Bukhari ya wakilci Najeriya a ta Duniya da akayi a Saudiyya.

