Hukumomin kasar Iran sun aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama’a kan wani mutum da aka samu da laifin kashe mutane hudu yan gida daya a garin Bayram, lardin Fars.
An rataye mutumin ne bayan kotun kolin kasar ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke masa.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka kashe sun hada da uwa da ‘ya’yanta guda uku a watan Oktoba bara.
Matarsa ma tana gidan yari bayan an same ta da hannu a cikin laifin, inda ake sa ran za a aiwatar da hukuncin kisa a kanta daga baya.
An gudanar da shari’ar ne bisa dokar Qisas ta Iran, wato duk wanda ya Kashe a kasheshi wacce ke bai wa iyalan wanda aka kashe damar zaben a rataye mai laifi, ko su karɓi diyya, ko kuma su yafe masa.
A kan haka iyalan sun nemi a aiwatar da hukuncin kisa kuma a bayyanar jama’a domin zama darasi ga wasu.
TST Hausa ta rawaito Kasar Iran na daya daga cikin kasashen da ke yawan gudanar da hukuncin kisa a duniya, inda mafi yawa ake yin su a bainar jama’a.

