Hukumar shari’a ta jihar Kano tayi karin haske kan labaran da akai ta yadawa cewa ta yanke hukunci game da sadakin Aure a jihar Kano.
Shugaban hukumar Malam Abbas Abubakar Daneji wanda ya yiwa manema labarai karin haske a ofishinsa ranar litinin 18 ga watan Augusta 2025 ,yace a taronsu na ranar Alhamis da ta gabata da hukumar zakka da Hubusi da kuma hukumar Hisba da sauran masu ruwa da tsaki sun tsayar da matsaya akan abinda ya shafi Zakka da diyar rai da kuma sadakin Aure a jihar Kano wanda jama’a suka fahimci batun ba daidai ba musamman sadakin Aure.
Sheikh Daneji yace da yawa daga cikin matasa,tsauwalawa wajen aure na hanasu yin aure ,hakan yasa hukumar shari’a da sauran Malamai suka zauna suka duba halin kunci da ake ciki suka tsayar da cewa za’a iya biyan naira dubu 20 a matsayin sadakin,sannan za’a iya biyan sama da haka.
Shugaban yace ya danganta da yarjejeniya tsakanin iyaye da ma’aurata.
“Shari’a ta yi tanadin cewa sadaki abu ne mai sauƙi wanda kowane matashi zai iya biya, ba tilas sai ya wuce kima ko ya zama abin da zai hana aure ba”Inji Malam Daneji.
Sheikh Daneji ya bada misali da ayoyin Alƙur’ani da hadisai da ke nuna cewa aure ya kamata ya kasance mai sauƙi.
Ya kawo hujja da maganar Manzon Allah (SAW) wanda ya ce mafi alheri daga cikin matan Musulmai su ne waɗanda sadakinsu ya fi sauƙi.
TST Hausa ta rawaito cewa a baya bayan nan anta cece kuce kan jita jitar da ake yadawa cewa hukumar shari’a ta Kano ta kayyade naira dubu 20 a matsayin mafi sadakin Aure a Kano.
A taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Alhamis,da ta gabata an yanke shawarar amincewa da naira dubu 20 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure,wanda hukumar shari’a tace anyiwa jawabin nata gurguwar fahimta.
Sai kuma naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure, da kuma naira dubu 985 a matsayin nisabin zakka, bisa lissafin farashin Durham.
Saidai Shugaban hukumar shari’a ta jihar Kano Malam Abbas Daneji yace babu Inda hukumar tace lalle dole naira dubu 20 za’a biya mafi karancin sadakin Aure,amma tana goyon bayan saukakawa a harkar auren.
Yace kafin fitar da wannan matsaya saida suka zauna da manyan malamai daga kowanne bangare ciki harda na jami’a.

