Jaridar Daily Truth ta gano cewa kimanin Naira biliyan 2.354 da ake kashewa a albashi da kuɗin gudanar da ofisoshin sanatoci 109 na Najeriya a kowane wata, ya isa a biya albashin farfesoshi 4,708 a jami’o’in ƙasar.
Tazarar albashi tsakanin masu mukaman siyasa da malamai a jami’a na ci gaba da zama abin muhawara a ƙasar.
A kwanakin baya, kafafen sada zumunta sun cika da hoton Farfesa Nasir Hassan-Wagini daga Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, wanda aka gani yana sayar da kayan lambu a kasuwar Batsari. Shi da wasu malaman jami’a da dama sukan yi wasu sana’o’i domin samun abin rayuwa.
Binciken Aminiya ya nuna cewa ana biyan farfesa matsakaicin albashi na ₦500,000 a wata, a yayin da sanata ke karɓar Naira miliyan 21.6 a wata.
A ranar 14 ga Agusta, 2024, Sanatan Kano ta Kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila ya shaida wa BBC Hausa cewa yana karbar albashin Naira miliyan 21.6 l a wata.
Ya ce, “Farfesa na karbar fiye da Naira miliyan 1 idan aka cire haraji da wasu kuɗaɗe, sai ya dawo Naira dubu ɗari shida. Amma kowanne sanata yana karbar Naira miliyan 21 a wata don gudanar da ofis,” in ɗan Majalisar Dattawan.
Bayanin nasa ya zo ne bayan Hukumar Tsara Albashi ta Ƙasa (RMAFC) ta ce sanatoci na karbar Naira miliyan 1.06 a wata a matsayin albashi da alawus.
Shugaban Hadaɗɗiyar Ƙungiyar Malaman Jami’a (CONUA), Dakta Niyi Sunmonu, ya ce malamai sun kasance a kan tsarin albashi ɗaya tun 2009, sai bara da gwamnati ta ƙara albashi da kashi 35% ga farfesoshi da kuma 25% ga sauran malamai.
Dakta Niyi Sumonu ya ce, “Albashin gaba ɗaya kimanin Naira dubu ɗari bakwai ne, amma bayan haraji da sauran cire-cire, sai ya koma ₦500,000.”
Ya ƙara da cewa farfesoshi ba za su iya samun rancen Naira miliyan goma zuwa miliyan 15 ba don sayen mota, duk da tsarin biyan bashin da ƙungiyoyin haɗin gwiwa da adashin fata ke bayarwa.
Ya bayyana cewa a shekarun 1960, farfesoshi su ne na uku girman albashi a Najeriya bayan Firayim Minista da Alƙalan Kotun Koli, sa’annan suna karɓar kuɗin gudanar da ofis da ’yan aiki.
“A yau, albashi ya tsaya cak fiye da shekara 16. Wasu malamai ba sa iya zuwa ofis kullum saboda rashin kuɗin sufuri. Wasu sau ɗaya suke zuwa a mako. Ba sa iya ƙarfafa ɗalibai kamar yadda ake yi a da,” in ji shi.
Sunmonu ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa, yana mai gargaɗi cewa jami’o’in Najeriya na fuskantar barazanar rushewa nan da shekaru 5 zuwa 10.
A wata hira da ta bazu a kafafen sada zumunta, Farfesa Balarabe Abdullahi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) Zaria ya ce albashinsa bai isa ya saka ɗansa a makaranta mai inganci a Abuja.
Ya gargaɗi cewa Najeriya na fuskantar barazanar rugujewar fannin ilimi idan ba a gyara tsarin ba.
Farfesa Samuel Agu na Jami’ar Jihar Abia ya ce yana dogaro da koyarwa a wasu jami’o’i da sana’o’i don cike giɓin buƙatu. “Albashina ya taɓa kaiwa ₦460,000, amma bayan haraji sai ya koma ₦390,000.
Yanzu ya kusa ₦490,000. Wannan shi ne gaba ɗaya, ba ni da wani alawus,” in ji shi.
Farfesa Chukwudi Ibe, Shugaba Tsangayar Adabi na Jami’ar FUTO ya ƙara da cewa, “Albashinmu ba ya isa. Hauhawar farashi ta cinye shi. Abin tausayi ne. Mu ne hasken al’umma, amma Najeriya ba ta ganin mu haka.
Malaman jami’an sun bayyana cewa barin ƙasar da abokan aikinsu ke yi domin neman rayuwa mai sauƙi a ƙasashen waje ya sa su ke fama da nauyin aiki mai yawa, wanda ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwarsu da jininsu.
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce wannan matsala ta ƙara ta’azzara sakamakon tsananin ƙuncin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar, inda malamai da dama ke kamuwa da cututtuka har ma da rasa rayukansu.
A watan Fabrairu 2024, ASUU ta bayyana cewa ta rasa mambobi 46 a yankin Abuja sakamakon matsin tattalin arziki da rashin ingantaccen albashi da yanayin aiki mara kyau.
Yankin Abuja ,ya ƙunshi Jami’ar Abuja da Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna; Jami’ar Tarayya, Lafia; Jami’ar Jihar Nasarawa, da Jami’ar Ibrahim Babangida, Lapai.
Cikin shekaru goma da suka gabata, malamai da dama sun bar ƙasar domin neman rayuwa mai sauƙi, lamarin da ya bar waɗanda suka rage cikin tsarin suna fama da nauyin aiki mai yawa.
Wadanda suka rage suna ƙara dare musu gwiwa a kullum saboda rashin albashi mai kyau da yanayin aiki mara kyau,” in ji Salahu Muhammed, mai kula da yankin Abuja na ASUU.
Ya kamata a lura cewa ƙungiyar ta rasa mambobi da dama a wannan lokaci sakamakon wahalhalun aiki, damuwa ta ƙwaƙwalwa da ta zuciya, da cututtuka masu alaƙa da waɗannan matsaloli. Misali, jami’o’in da ke yankin Abuja sun rasa mambobi 46.
A gaskiya, kwana biyu da suka gabata, ƙungiyar ta rasa wani shahararren Farfesa a fannin Kifi, Farfesa Johnson Oyero daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna, sakamakon rashin samun ingantaccen magani,” in ji Salahu.
A kwanakin baya, an ƙaddamar da gidauniya tarl naira miliyan 13 don biya wa Farfesa Abubakar Roko na Sashen Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato (UDUS) kuɗin magani.
Duk da gudummawar da aka tara, ciki har da naira miliyan 5 daga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Farfesa Roko ya rasu daga bisani.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa a Najeriya ne malamai ke samun ƙarancin albashi fiye da sauran ƙasashen duniya.

