Jam’iyyar NNPP a Kano ta yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen Kano ta sanar ba a zabukan cike gurbi na kananan hukumomin Tsanyawa da Ghari, inda ta yi zargin cewa an shirya makirci da murdiya domin amfanar da jam’iyyar APC.
A wani taron menema labarai da shugaban jam’iyyar a Kano,Dr Hashimu Sulaiman Dungurawa ya kira yace hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke ya wajabta gudanar da sabon zabe a mazabu goma, amma INEC ta yi watsi da hakan, ta kuma sanar da sakamakon da aka wasu suka mika mata.
Jam’iyyar ta bayyana wannan a matsayin rashin adalci da kuma kwace kuri’un jama’a, tare da zargin hukumar zabe da keta doka ta hanyar soke zabuka daga hedikwatarta maimakon a wuraren tattara sakamakon.
Sai dai a daya hannun, NNPP ta yaba da yadda aka gudanar da zaben cike gurbi a Shanono da Bagwai, inda ta ce an yi sahihin zabe kuma jama’a sun zabi ‘yan takararta cikin kwanciyar hankali.
Jam’iyyar ta gode wa masu kada kuri’a da jami’an tsaro saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya yayin zabukan.
Dungurawa ya jaddada cewa NNPP za ta ci gaba da kare muradun al’umma tare da yakar duk wani yunkuri na murde zabe ko amfani da karfin gwamnati domin tauye ‘yancin jama’a.

