Tsohon Shugaban Kasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya fara shirin amincewa da bukatar da jam’iyyar PDP ta gabatar masa na tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2027, kamar yadda wani amintaccensa kuma makusancinsa ya tabbatar.
Rahotanni daga manyan kafafen yada labarai na Najeriya sun bayyana cewa Jonathan ya yanke shawarar tsayawa takara ne sakamakon damuwar da yake da ita kan tsananin talauci da matsin rayuwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta a karkashin mulkin jam’iyyar APC mai ci.
Wata majiya daga jam’iyyar PDP wacce ta nemi a boye sunanta ta shaidawa jaridar Vanguard cewa tsohon shugaban kasa ya fara ganawa da manyan shugabanni daga Arewacin Najeriya da sauran sassan kasar nan domin neman goyon baya kafin sanar da takararsa a hukumance.
Jonathan ya mulki Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015 ,Inda a yanzu idan har ya bayyana aniyarsa ta takara a hukumance kuma yayi nasara to zaiyi wa’adin mulkin daya ne.
Tun a zaben 2019 akaita neman Jonathan din ya fito takara amma ya na zamewa.
Jaridar Aljazirah News ta bayyana cewa Jonathan ya shirya tsaf domin komawa tunkarar takarar shugaban kasa, tare da samun goyon baya daga wasu manyan jiga-jigan siyasa.
TST Hausa ta rawaito cewa sakataren kudi na kasa na jam’iyyar PDP ya ce Jonathan na iya samun tikitin takara kai tsaye daga jam’iyyar.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke fara shiri tsaf domin babban zaben 2027, inda ake kallon dawowar Jonathan a matsayin wani gagarumin mataki da zai canza akalar siyasar kasar nan.
Rahotanni kuma sun nuna yadda akai ta yada hotunan Jonathan da Sanata Rabiu Musa kwankwaso a shafukan sada zumunta na zamani,Inda ake wallafa cewa Jonathan zaiyi takarar Shugaban kasa shi kuma Kwankwaso mataimakinsa ,saidai a hukumance ba’a tabbatar da Labarin ba.

