Gidauniyar Atiku Abubakar ta bai wa wasu ‘yan mata uku daga Najeriya guraben karatu na cikakken kudin makaranta, bayan da suka yi fice a gasar iya Turanci ta duniya ta kananan yara mata wato TeenEagle Global Finals.
Wadanda suka samu wannan gagarumar nasara sun hada da Nafisa Abdullahi, Rukaiya Fema, da Khadija Kalli, wadanda suka wakilci Najeriya a gasar da aka gudanar a matakin kasa da kasa.
A wata sanarwa da gidauniyar ta fitar, an bayyana cewa guraben karatun na daga cikin kokarinta na tallafa wa matasa masu hazaka tare da inganta ilimi, musamman ga ‘yan mata.
Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara bukatar bai wa matasa damammaki, domin su kasance shugabanni masu tasiri a nan gaba.
Gasar TeenEagle Global Finals 2025 an gudanar da ita ne a birnin London, United Kingdom, kuma an kammala ta ranar 3 ga Agusta, 2025 .
TST Hausa ta gano cewa a bana an samu babban juyin zamani a wannan gasa Inda ‘yar shekara 17, Nafisa Abdullah Aminu daga jihar Yobe,a Najeriya, ta lashe gasar, a karo na farko inda ta doke ‘yan takara daga ƙasashe 69 kuma ta kasance ta fi kowa ƙwarewa a fannin harshen Turanci
TST Hausa ta rawaito cewa hakan na zuwa ne bayan kiraye kirayen da wasu daga cikin al’ummar Arewacin Najeriya sukayi na lalle gwamnatin tarayya da sauran yan siyasa da attajirai su taimaki daliban da suka nuna kwazo kamar yadda Shugaban kasa Bola Tinubu ya gwangwaje yan wasan kwallon kafa mata da kuɗade da gidaje da Lambobin yabo.

