Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta sanar da shirin gudanar da wa’azi da taron faɗakarwa ga mazauna gidan ajiya da gyaran hali na Janguza da kuma gidan kula da yara na Nassarawa, domin tallafa musu da kuma inganta tarbiyya da gyaran halayensu.
Shugaban hukumar, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar aiki da suka kai gidan gyaran halin na Janguza a ranar Laraba.
Ya ce wannan shiri na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin aiwatar da umarnin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na rage raɗaɗin rayuwa da ƙarfafa kyawawan dabi’u ga mazauna irin waɗannan cibiyoyi.
Shugaban yace karanto musu wa’azi mai ratsa zuciya zaisa su rika tuna hukuncin Allah akansu.
Baya ga Janguza, tawagar hukumar ta kuma kai ziyara gida uku na kula da mutane masu buƙata ta musamman: gidan gyaran hali na Goron Dutse, gidan kula da yara na Nassarawa, da kuma gidan kula da masu larurar tabin hankali na Tudun Maliki.
A yayin ziyarce-ziyarcen, hukumar ta raba tallafin abinci da abin sha da suka haɗa da dafaffen abinci ga mutum 400, lemo, ruwa, da kuma kayan marmari irin su lemon zaƙi, kankana da abarba, domin sauƙaƙa musu rayuwa da kuma ƙara ƙarfafa jin daɗi da kwanciyar hankali.
Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya ce ziyarar wani bangare ne na kokarin hukumar na ƙarfafa zaman lafiya da haɓaka haɗin kai da jinkai a cikin al’umma.
Shugaban gidan gyaran hali na Janguza, DCC Ɗanlami Inuwa, ya yaba da wannan mataki na hukumar, yana mai kira ga sauran al’umma da su rinƙa kai ziyara da tallafi ga gidajen gyaran hali, domin bayar da gudunmawa ga gyaran ɗaurarru.
Shi ma a nasa ɓangaren, mataimakin shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali a jihar Kano, AC Kafilu Abdullah Nassarawa, wanda ke kula da gidan na Goron Dutse, ya nuna godiyarsa bisa wannan ziyara da tallafi, yana mai cewa hakan na da matuƙar tasiri wajen rage damuwa da haɓaka kwanciyar hankali a tsakanin mazauna gidajen.
Shugaban hukumar Shari’a Sheikh Abbas Abubakar Daneji ya jagoranci tawagar ziyarar, tare da rakiyar Kwamishinoni biyu Gwani AbdulHadi Ɗahiru Yakasai da Sheikh Ali Ɗan Abba da daraktoci da wasu muhimman jami’an hukumar

