Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da daukar matasa 1,038 aiki a matsayin ma’aikatan Extension Services a bangaren noma, a wani babban yunkuri na habaka fannin noma da kuma rage rashin aikin yi a tsakanin matasa a jihar.
An kaddamar da shirin daukar aikin ne a wani taro na musamman da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano inda gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin muhimman manufofin gwamnatin sa na farfado da tattalin arzikin jihar ta hanyar bunkasa noma, da kuma karfafa gwiwar matasa su shiga harkokin noma na zamani.
A cewar gwamna Yusuf,daukar sabbin ma’aikatan zai shafi dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, kuma za su rika bada horo ga manoma a matakin ƙasa, musamman a karkara, domin kara yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci a jihar.
“Wannan matakin da muka dauka na daukar matasa fiye da dubu guda a bangaren aikin noma, ba wai kawai zai taimaka wajen samar da ayyukan yi bane, har ila yau zai taimaka wajen jawo hankalin matasa su rungumi noma a matsayin sana’a mai daraja da riba,” inji gwamnan.
Ya ce gwamnati za ta horas da sabbin ma’aikatan yadda ya kamata, tare da samar musu da kayayyakin aiki da motocin hawa, domin saukaka musu wajen gudanar da aikinsu a cikin al’umma.
Haka zalika, gwamnan ya bayyana cewa gwamnati na da shirin fadada filayen noma da kuma farfado da madatsun ruwa domin tabbatar da noma yana gudana duk shekara ba tare da dogaro da ruwan sama kadai ba.
Yace wannan shiri na daukar ma’aikatan ya samu goyon bayan masana harkar noma,da kungiyoyin manoma da kungiyoyin matasa, wadanda suka yaba da matakin da gwamnatin Kano ta dauka, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen rage zaman kashe wando da samar da ci gaba mai dorewa.
Daga karshe, gwamna Yusuf ya bukaci sabbin ma’aikatan da su kasance jakadu na kwarai a fannin noma,sannan su nuna gaskiya,da jajircewa da kishin kasa a cikin aikin da aka dora musu.

