Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba ’yan wasan kwallon kwando na mata na Najeriya, D’Tigress, lambar girmamawa ta kasa tare da kyautar kudi har dala $100,000 ga kowacce ’yar wasa.
Shugaban ya kuma baiwa kowanne memba na jami’an horarwa da ma’aikatan fasaha na kungiyar dala $50,000. Baya ga haka, an kuma bai wa duka ’yan wasa da jami’an horarwa gidaje ko filaye a birnin tarayya Abuja.
Wannan karramawar ta biyo bayan nasarar da D’Tigress suka samu na lashe gasar AfroBasket 2025 da aka gudanar a Côte d’Ivoire, inda suka lashe kofin karo na bakwai a tarihin su, da kuma karo na biyar a jere ba tare da faduwa ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da aka shirya a fadar shugaban kasa, Aso Rock, a ranar Lahadi, 4 ga Agusta, 2025, inda ya yaba da kwazonsu da sadaukarwar da suka nuna don ganin Najeriya ta ci gaba da zama zakaran Afrika a fagen kwallon kwando na mata.
Baya ga kudin, kowacce ’yar wasa ta samu lambar Officer of the Order of the Niger (OON) daya daga cikin manyan lambobin girmamawa a Najeriya.
Wannan lamari ya nuna irin goyon bayan da Gwamnatin Tinubu ke nunawa ga mata da kuma ci gaban wasanni a Najeriya, musamman bayan irin wannan karramawa da Super Falcons suka samu a baya.
D’Tigress sun kafa tarihi da lashe AfroBasket karo na 7, suna ci gaba da mulkin Afrika a kwallon kwando na mata.

