Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na tattara bayanai da kuma rajistar manoma a dukkan fadin Najeriya.
Wannan matakin na daga cikin kokarin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi domin dakile hauhawar farashin abinci a kasar nan.
Dada Olusegun ya wallafa X cewa karamin ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka a ranar Laraba a taro da aka yi a Kaduna.
Sanata Abdullahi ya ce sabuwar rajistar za ta taimaka wajen kawar da ‘yan damfara da ke karbar tallafin noma ba tare da cewa suna da gonaki ba.
Ministan noma ya ce rajistar manoman za ta bai wa gwamnati damar tantance wadanda ke aikin noma na hakika, da kuma tabbatar da cewa su kadai ke cin gajiyar tallafin gwamnati.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta himmatu wajen kara samar da abinci da saukaka farashi ta hanyar daukar matakai na gaggawa da kuma na dogon lokaci.
Rahotanni nacewa umarnin da shugaba Bola Tinubu ya yi na daga cikin shirinsa na sanya dokar ta-baci a bangaren samar da abinci.
Ministan ya ce gwamnati na shirin tallafa wa manoman shinkafa har 44,500 tare da ba su horo da kuma samar da manyan injina na zamani da za su taimaka wajen kara yawan amfanin gona.
Sanata Abdullahi ya bayyana cewa an kawo motacin noma kirar tractor 2,000 daga kasar Belarus da kuma kayayyakin aikin noma 9,000 domin tallafa wa manoma a fadin kasar nan.

