Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙara wa babban kontirola na hukumar hana fasa kauri ta Najeriya Bashir Adewale Adeniyi, shekara ɗaya a kan kujerarsa.
Tun da farko ana sa ran wa’adinsa zai ƙare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025, amma yanzu zai ci gaba da jagoranci har zuwa Agusta, 2026.
A cewar wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayani da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, an ƙara wa’adin ne domin bai wa Adeniyi damar kammala sauye-sauyen da ake aiwatarwa da kuma wasu muhimman tsare-tsare na gwamnatin Tinubu.
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaba Tinubu yana yaba wa jagoranci na kwazo da Aminci da Adeniyi ke nunawa, kuma yana da tabbacin cewa wannan ƙarin lokaci zai ƙarfafa ayyukan Hukumar Kwastam wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Tinubu ya naɗa Adeniyi a matsayin Shugaban Kwastam a watan Oktoban 2023 bayan rike mukamin a matsayin mai riƙon gado tun daga watan Yunin shekarar nan, bayan saukar Hameed Ali.

