Shugaban rukunin kamfanonin yada labarai na Vision FM a Najeriya, Alhaji Umar Farouk Musa, ya amince da nadin Malam Anas Idris Hassan a matsayin shugaban gidan rediyon Vision FM dake Kano.
Nadin nasa ya biyo bayan jajircewa da kwarewar da Malam Anas ya nuna a tsawon shekarun da ya shafe yana aikin jarida, musamman a fannin rediyo da talabijin.
A wata ganawa da sabon shugaban, Anas Idris Hassan ya yi da TST Hausa, ya bayyana godiyarsa ga duka ‘yan uwa da abokan aiki da suka kasance tare da shi a baya, inda ya roki al’umma da su ci gaba da yi masa fatan alheri da addu’o’in samun nasara a koda yaushe.
Ya mika takardar ajiye aiki a yammacin Alhamis 31 ga watan Yuli 2025 ga hukumar gudanarwa ta Rahma Radio da Talabajin Kano.
Ya kuma nuna godiya ta musamman ga shugabar hukumar zartaswa ta tashohin Rahma Radio da Talabijin, Hajiya Binta Sarki Mukhtar, saboda damar da ta ba shi a baya, da kuma Shugaban Sashen Mulki na gidan Rahma Radio,da Talabajin Alhaji Salisu Idris Yakasai bisa gudummawar da ya bashi tun daga lokacin da ya fara aikin zuwa wannan lokaci.
Anas Idris Hassan ya fara aikinsa na jarida ne a tashar Freedom Radio Kano (99.5 FM) a shekarar 2006 a matsayin ɗan jarida mai zaman kansa (freelancer) inda ya gabatar da wani shirin harshen larabci wato Mazeekah.
A shekarar 2011 ne, ya koma Rahma Radio a hukumance, inda ya ci gaba da gudanar da aikinsa a matsayin mai aiko da rahoto daga ofishin mataimakin gwamnan jihar Kano, kafin daga bisani ya zama wakilin Rahma Radio a ofishin Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2015.
A tsawon zamansa a Rahma Radio ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da: Editan Labarai (News Editor), Mai karanta labarai (News Caster), Mai tsara shirye-shirye (Producer), ciki har da shirin Fatawowin Rahma tare da Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo, Mai fassara (Translator) musamman daga Turanci zuwa Hausa da kuma Larabci, sai gabatar da shirin “Munawwatul Arab” shiri na karshen mako da ke sada zumunta da masu jin Larabci.
Daga bisani ya zama Shugaban Sashen Labarai da Al’amuran Yau da Kullum na Rahma Radio da Talbijin.
Anas Idris Hassan ya shahara a fagen aikin jarida da yaɗa labarai tare da gagarumar ƙwarewa a kafafen rediyo da talabijin, yana kuma da kyakkyawar fahimta a fannoni da dama na aikin yada labarai.
A yanzu haka, ya karɓi ragamar jagorancin Vision FM Kano da kwarin guiwar ci gaba da gina ingantaccen gidan rediyo da zai ci gaba da hidimtawa al’umma.
Sabon GM din zai fara aiki 1 ga watan Augusta 2025.

