Wasu ƴan kasar Ghana sun gudanar da zanga-zanga da ke nuna ƙiyayya ga ƴan Najeriya, musamman ma ƴan kabilar Igbo, inda suka zarge su da aikata laifuka masu tayar da hankali kamar fyaɗe da karuwanci, kisa ta hanyar asiri, da kuma garkuwa da mutane.
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ranar Talata, masu zanga-zangar suna dauke da alluna da rubuce-rubuce kamar haka:
“A daina fashi da makami da kai hari,”
“Lafiyarmu na cikin hadari saboda yawon karuwanci,”
“Su waye ke kare hakkin ƴan Ghana?”
“Ƴan Najeriya na sace mutane suna amfani da su don asiri,”
“Ƴaƴanmu na bacewa saboda Igbos.”
Wasu sunyi rubutu cewa duk wanda bai fita daga kasar ba a bakin ransu.
Masu zanga-zangar sun kuma nuna hoton wani mutum da ake zargin wani dan Najeriya ne da ya kashe a yankin Accra.
Wata mace cikin masu zanga-zangar ta ce: “Ƴan Najeriya dole su tafi,su bar kasar domin ba za ka zauna a ƙasar wani kana bin son ranka ba.
Wani mahalarta zanga-zangar ya kara da cewa: “Ƴan Najeriya, musamman Igbos, sun mamaye kasuwanninmu kuma suna aikata miyagun ayyuka. Suna da wani sarki na Igbo a Ghana ma. Sun kwace ƙasashenmu.”
Wannan lamari ya tunatar da matakin gwamnatin Najeriya a shekarar 1983 lokacin da shugaban kasa Shehu Shagari ya bayar da umarnin korar kusan mutane miliyan biyu na bakin haure, galibinsu ƴan Ghana ne, daga Najeriya.
Wannan ya haifar da shahararriyar jakar “Ghana Must Go” da mutane ke amfani da ita wajen kwashe kayansu.
A halin yanzu, babu wani jawabi daga gwamnatin Ghana game da wannan matsala ko matakin da za a ɗauka kan rikicin da ke tasowa tsakanin jama’ar kasashen biyu.
Haka zalika, gwamnatin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa ba.
Masana da masu lura da al’amuran yanki suna nuna damuwa kan yadda rikicin zai iya zama barazana ga haɗin kan kasashen yammacin Afirka, musamman ma a cikin ECOWAS, da ke goyon bayan yancin zirga-zirgar mutane da kaya.
Ana bukatar diplomasiyya, tsauraran matakan doka, da kuma ilimantar da jama’a don hana rikicin yaduwa ko rikidewa zuwa tashin hankali tsakanin ƴan Najeriya da ƴan Ghana.

