Tsohon Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC kuma Shugaban hukumar gudanarwar Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Attahiru Jega ya nuna takaicinsa kan yadda jami’o’in Najeriya suka dukufa wajen karrama mutane marasa ilimi da digirin girmamawa saboda wata bukata ta kashin kai ba domin martaba ilimi ba.
Farfesa Jega ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayinsa na shugaban taron laccar yaye dalibai karo na 14 na jami’ar Open university dake Abuja a yammacin juma’ar yau 11 ga watan Afirilun 2025.
Jega wanda ya jinjinawa daliban da suka sadaukar da lokacinsu wajen kammala karatun da sukayi a jami’a a Najeriya,yace babban kuskure ne dalibi ya bata lokacinsa shekara hudu ko sama da haka a cikin Aji ,haka shima malami ya bata lokacinsa wajen yin bincike ,amma rana daya a samu wata jami’a a Najeriya ta karrama wani mara Ilimi wanda ko hanyar aji bai sa ni ba da digirin girmamawa.
Hakan zubar da mutunci da martabar ilimin jami’oi ne a Najeriya.
Farfesa Jefa ya kara dacewa hakan na daga cikin abinda yake zubar da kima da neman ilimi a Najeriya.
Ya kuma karfafa guiwa tare da zaburar da dalibai,a Najeriya da malamai da ma’aikata kan su dage wajen farfado da darajar ilimi da kuma kyamatar yadda ake karrama mutanan da basu taba shiga aji ba saboda siyasa ko kuma biyan bukatar kashin kai.
Anasa jawabin Shugaban Bankin Raya kasahen Nahiyar Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina ya gabatar da jawabi a wajen taron laccar yace a baya yawancin yan ƙasashen duniya suna alfahari da ilimin da ake samu a Najeriya,yana mai cewa har yanzu wannan martabar tana nan ga Najeriya.
Saidai yayi gargadin cewa siyasa na neman mayar da hannun agogo baya idan ba’a yi takatsantsan ba.

