Shugaban jam’iyyar APC na Najeriya Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cewa shugaba Bola Tinubu zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu sannan ya mikawa yan Arewa.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin yan Kungiyar yada manufofin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da kuma kungiyar matasan APC na shiyar Arewa a ofishinsa dake sakatariyar jam’iyar APC na kasa a Abuja.
A cewarsa, zai zama rashin adalci idan aka hana shugaban kasa Tinubu damar sake tsayawa takara bayan an baiwa wani dan Arewa irin wannan damar ya kammala wa’adinsa na shekaru 8 a tsakanin 2015 zuwa 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kano Dr.Ganduje ya yi alkawarin cewa jam’iyyar APC za ta cigaba da bin tsarin shiyya-shiyya, tare da tabbatar da cewa an kiyaye da tsarin karba karba tsakanin Kudu da Arewa.
Ya ce, a “lokacin da wani shugaban yankin Arewacin kasar nan ya yi mulkinsa na tsawon shekaru takwas, mun ba da shawarar cewa shugaban jam’iyyarmu ya fito daga Kudu haka kuma idan Shugaban kasa ya fito daga kudu haka shima Shugaban jam’iya zai fito daga Arewa”,Inji Ganduje
Ganduje, ya kara dacewa ya amincewa da manufofin Shugaba Tinubu, inda ya bayyana cewa tuni kasar nan ta samu sakamako mai kyau, musamman a fannin tattalin arziki.
TST Hausa ta rawaito ce a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2024 ne maganar Sakataren gwamnatin tarayya George Akume ta tada kura bayan ya nemi masu son zama Shugaban kasa daga Arewa a shekarar 2027 da su dakatar da aniyarsu har sai Bola Ahmad Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara 8

