Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya ce ko duka gwamnonin Najeriya zasu koma APC hakan ba zaisa su Karaya a kokarinsu na kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 ba.
Ya ce su a cikin ƙungiyarsu ta masu haɗaka sun fi mayar da hankali ne kan talakawa, ba shugabanni ba.
Ƙungiyar masu haɗakar ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar, da Peter Obi, da Nasir El-Rufai ta zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su kara da APC a zaɓen 2027.
Sun nemi al’ummar Najeriya da su mara musu baya domin ceto Kasar daga hannun yan Jari hujja.
David lawan ya kuma tabbatar da cewa akwai jigan jigan yan siyasa anan gaba da zasu shigo tafiyar.
A wata ganawarsa da manema labarai a Abuja Shugaban jam’iyar ADC na kasa Dr. Ralphs Okey Nwosu yace nan da mako daya ko biyu zasu kammala tattaunawa ta karshe ta hadaka domin tunkarar APC a 2027.
Yace ADC tana da farin jinin da zata kayar da APC a zaben 2027.

