Yan Majalisar Wakilai sun amince da sabon tsarin da ya ƙara yawan Kuɗaden da ɗan takarar shugaban ƙasa da na gwamna za su iya kashewa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2026.
Bisa wannan tsarin, ɗan takarar shugaban ƙasa zai iya kashe har naira biliyan 10, yayin da ɗan takarar gwamna zai iya kashe naira biliyan 1 zuwa 3.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/majalisar-wakilai-na-maraba-da-duk-wata-doka-zata-inganta-walwalar-yan-jarida-a-najeriya-abbas/
Majalisar ta bayyana cewa wannan gyara na nufin baiwa ɗan takara damar gudanar da yakin neman zabe yadda ya kamata a duk fadin ƙasa, tare da tabbatar da gaskiya da adalci a harkar siyasa.
Masu sharhi sun yi nuni cewa ƙarin kuɗin na iya taimaka wa ɗan takara wajen gudanar da ayyuka masu tasiri, amma sun jaddada bukatar tsauraran matakai wajen amfani da kuɗaɗen yakin neman zabe domin gujewa cin hanci da rashawa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/majalisar-wakilai-na-neman-jihohin-najeriya-su-koma-67-ta-lissafo-karin-31-da-zaa-samar/
TST Hausa ta rawaito cewa a yakin neman zaben 2023 an kayyadewa dan takarar Shugaban ƙasa ya kashe naira biliyan 5 yayinda gwamna zai kashe naira biliyan 1 sai dan takarar majalisar dattawa zai kashe naira miliyan 100 sai kuma dan takarar majalisar wakilai zai kashe naira miliyan 70 sai kuma dan takarar majalisar jiha naira miliyan 30.

