Kamfanin Meta ya fara cire kananan yara yan kasar Australia ‘yan ƙasa da shekara 16 daga dandalin Instagram da Facebook da Threads, mako guda kafin fara dokar haramta wa matasa amfani da kafafen sada zumunta.
An fara sanar da ƴan shekaru 13 zuwa 15 cewa za a rufe shafukansu daga yau 4 ga Disamba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yanzu-yanzufadar-shugaban-kasa-ta-nesanta-kanta-da-labarin-sauke-farfesa-mahmud-daga-shugaban-inec-da-maye-gurbinsa-da-
Ana sa ran wannan mataki zai shafi kusan masu amfani da facebook yara 150,000 da Instagram yara 350,000.
Dandalin Threads kuwa ba za a iya amfani da shi kai tsaye ba sai ta dandalin Instagram.
Dokar ta Australia, wacce ta zama ta farko a duniya, za ta fara aiki daga 10 ga Disamba, inda kamfanoni za su iya fuskantar tarar har dala miliyan 45 idan suka kasa daukar matakan da suka dace domin hana yan ƙasa da shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta.
Meta ta bukaci gwamnati ta tilasta wa rumbun manhajoji tabbatar da shekaru kafin sauke wata manhaja tare da samun amincewar iyaye ga ‘yan ƙasa da 16, domin hakan zai kawar da buƙatar tabbatar da shekaru a kowanne manhaja.
Sauran kafafen sada zumunta da wannan dokar ta shafa sun haɗa da YouTube da X da TikTok da Snapchat da Reddit da Kick da Twitch.

