Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske game da kiran da babban hafsan hafsoshin kasar, Janar Christopher Musa, ya yi, cewa jama’a su fara tunanin koyon dabarun kare kansu da aka amince da su a duk fadin duniya.
Hedikwatar ta ce jama’a sunyiwa kiran na Musa gurguwar fahimta wata Inda tace babu Inda babban jami’in tsaron ya bada umarnin ga mutane su dauki makami su kare kansu ,saidai yana nufin su koyi abubuwa kamar kokawa da judo da dambe da ninkaya da iya tukin mota da dai sauransu domin kare kansu daga yan bindiga.
Birgediya Janar Tukur Gusau, wanda shi ne daraktan yada labarai na rundunar tsaron Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa shi babban hafsan tsaron na nufin a matsayinka na dan adam bai kamata ka zauna haka kawai ba tare da ka koyi wata dabara da za ka iya kare kanka ba.
Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar, ya ce,ya kamata jama’a su sani Janar Chiristopher Musa, bai yi Magana a kan mutane su kare kansu daga hare haren’yan bindiga ba, maganar da ya yi itace su kare kansu daga wasu abubuwa na yau da kullum.
TST Hausa ta rawaito cewa Janar Tukur Gusau, ya ce akwai wasu kasashen duniya da suka koyi irin wadannan dabarun kuma ya zama dole yan Najeriya suyi koyi domin kare kansu da kansu daga barazanar tsaro.
Acewar sanarwar wannan rashin fahimta a game da kalaman babban hafsan hafsoshin tsaron na Najeriya ya samo asali ne bayan da ya shawaraci ‘ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.
C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a ranar Alhamis 21 ga watan Augustan 2025.
Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.
Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya.

