Dan gwagwarmaya kuma dan Jarida mai wayar da kan jama’a a kano ya roki hukumar Hisba ta jihar Kano da malaman Addinin musulunci su fito su taka burki kan yadda ake siyasar batanci da dabbanci a Kano.
Anas Idiris Hassan daya daga cikin yan jarida a Kano, wanda ya nuna bacin ransa a yayinda yake zantawa da wakilin TST Hausa yace ba’a taba shiga wani yanayi na batanci ga juna da taba mutunci juna a siyasa ba sama da wannan lokacin kuma abin yafi kamari a Kano.
Yace mutukar Malaman musulunci sukayi Allah wadarai da batun akan mumbari ko wajen karatuka kan halin yan siyasar dake maida hankali wajen batanci ga juna,to zasu rage ko ma su daina.
Sai kuma Hukumar Hisba karkashin jagorancin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da yace akwai rawar da zata taka akan irin wadanan mutane da suke kiran kansu yan siyasa suna zubarwa mutanan Kano mutunci a idanun duniya.
“Abinda muke tsoro shine kada Allah yayi fushi da mutanan Kano saboda wawayen cikinmu ,wasu su janyowa wasu ,kamar yadda Allah ta’ala ke cewa “Kuji tsoron saukar musufar da wasunku zasu janyo ta sauka akanku kuma ta shafi har wadanda babu ruwansu.”
Malam Anas Idiris Hassan yace babban laifi ne a rika amfani da shafukan sada zumunta na zamani wajen jifan juna da aikata LUWADI a gari kamar kano,sai yace “Wa iyazubillah “Anas yace kalmar ko dadin fada babu akan harshen musulmi.
Ya kara dacewa mutukar ba’a taka burki ga irin wadannan yan siyasa a Kano ba ,to zasu ci gaba da zubar da mutuncin Kano din mai cike da malamai da mutanan kirki a cikinta.
Ya shawarci yan siyasa suyi siyasarsu,amma idan ta hada da jifan juna da munanan kalamai musamman kalamar LUWADI ,da ZINA da KARUWANCI da ZAGE ZAGEN IYAYE “to a jira aga fushin da Allah zaiyi da mutane mutukar ba’a dakatar kuma an tuba ba.
Hassan ya nemi hukumar Hisba ta Kano da majalisar malamai ta Kano da Malaman Addinin musulunci su fito su bayyana matsayinsu akan wadannan munanan kalamai da yan siyasa ke jifan juna dasu a kafafen sadarwa na zamani.
TST Hausa ta rawaito cewa tun a karshen watan Janairun shekarar 2025 yan siyasar Jihar Kano daga bangaren Kwankwasiyya da Gandujiyya ke jifan juna da kalmar ta Luwadi a tsakaninsu.
Dan gwagwarmayar Anas yace babban abin tsoro shine kada kananan matasa da yara masu tasowa su dauka abinda sukeyi daidai ne ,ga kuma ana fuskantar azumin Ramada na bana,amma su yan siyasar sun bige da cin mutuncin juna.
Abin jira a gani shine ko majalisar malamai ta Kano da hukumar Hisba zasu magantu ko kuwa.

