Wani babban Lauya a Najeriya mai mukamin (SAN), Muhammad Ndarani, ya bukaci ‘yan Najeriya duk matsayin da mutum yake dashi da ya koma gona domin noma abinda zaici shida iyalansa
Lauyan yace matukar mutum yafi karfin abinci a gidansa to ya fita daga kunci rayuwa da ake ciki da kaso a kalla 70 cikin dari.
Barista Ndarani ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja.
Lauyan ya kuma fusata da rahoton da aka fitar cewa akalla ‘yan Najeriya miliyan 26 da dubu dari biyar ne suka fuskanci matsalar karancin abinci a shekarar 2024 da take karewa sakamakon noman da ba a iya yi ba saboda matsalar tsaro da Kuma ambaliyar ruwa da akasha fama da ita.
Lauyan yace abinda ya hango nan gaba , matukar gwamnatin tarayya da jihohi basu gyara ba matsalar karancin abinci kara kamari takeyi ba tare da yawancin mutane sun gane ba .
Yace a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa kuma ake kara tara iyali ya kamata kowa ya mallaki gonar noma dan samar da wadataccen abinci a ƙasar nan .
“Dole ne mu koma noma, a bar masu hannu da shuni su shiga harkar noma na gaskiya kamar yadda Gwamna Bago ke yi a jihar Neja yayin da kananan manoma ke iya noma ko da iya abinda zasuci ne .
Ndarani ya ce ‘yan Najeriya na sa ran jami’o’in kasar nan za su samar da sakamakon bincike kan amfanin gona mai jure yanayi, inganta tsarin kula da ruwa da inganta aikin noma mai dorewa.

