Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta yi kakkausar suka kan kasafin kuɗin da gwamnatin tarayya ta ware wa ɓangaren lafiya a shekarar 2026.
Kungiyar ta ce , adadin kudin bai dace da halin da tsarin kiwon lafiyar ƙasar nan ke ciki ba.
A cewar ƙungiyar, kasafin lafiyar da aka tsara na naira tiriliyan 2 da kusan rabi idan aka raba shi daidai da yawan jama’ar Najeriya, yana nufin kimanin naira dubu 10 da dari hudu ne kacal kowane ɗan ƙasa zai amfana a shekarar 2026.
Sannan adadin ya nuna a duk wata naira 870 ne Kowanne dan Najeriya zai amfana, adadin da NMA ta ce ba zai iya biyan mafi ƙarancin buƙatun lafiya ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-ya-amince-da-karin-shekaru-barin-aiki-ga-likitoci-da-maaikatan-lafiya-na-najeriya/
NMA ta bayyana cewa ƙarancin kuɗin na ci gaba da shafar ayyukan asibitoci,da samar da magunguna da kayan aiki, tare da raunana walwalar ma’aikatan lafiya, lamarin da ke haddasa yajin aiki da kuma ƙara yawan likitocin da ke barin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta kuma nuna cewa kasafin lafiyar na wakiltar ƙasa da kashi 5 cikin 100 na kasafin ƙasa baki ɗaya, alhali Sanarwar Abuja ta 2001 ta tanadi cewa ƙasashen Afirka su ware aƙalla kashi 15 cikin 100 na kasafinsu ga ɓangaren lafiya.
NMA ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba kasafin, tare da ƙara yawan kuɗin da ake warewa lafiyar jama’a zuwa aƙalla kashi 10 cikin 100, domin ceto tsarin kiwon lafiya daga durƙushewa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-jigawa-da-likitocin-najeriya-mazauna-saudiyya-sun-duba-masu-lalurar-idanu-dubu-4-kyauta-a-jigawa/
A nasa ɓangaren, Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce gwamnati na da niyyar ƙara kaso na kasafin lafiyar zuwa kusan kashi 6 cikin 100, wanda zai kasance mafi girma cikin shekaru da dama.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da su ƙara saka hannun jari a ɓangaren lafiya, musamman a asibitocin kula da lafiya na matakin farko.

