Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya amincewa Falasɗinawa 1,000 da su shiga kasar su sauke farali kyauta a aikin Hajjin bana da za’a gudanar a Kasar.
Sarkin ya dauki wannan matakin ne ga Falasdinawa a wani yunkurin jin kai ga ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza.
Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin.
Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke ciki sakamakon yaƙi da ƙasar Yahudawa ta Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza.
Ya nemi Falasdinawan da su yiwa yankinsu adu’a da kuma yan uwansu da suka mutu a yakin da ya faru

