Ministan lafiya lafiya na Najeriya Farfesa Muhammad Pate shine ya bayyana hakan a wajen kaddamar da kwamatin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a birnin tarayya Abuja .
A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na ma’aikatar lafiya ta Najeriya Alaba Balogun ya fitar yace ministan ya nuna damuwa akan makuden kudaden da cutar ke lashewa duk shekara
Yace basu kallon cutar a matsayin hadari ga al’umma kadai ,ana kallonta a matsayin wacce ke rusa tattalin arzikin kasa .