Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce matashin da ya yi yunkurin tunkarar shugaban kasa Bola Tinubu lokacin da yake jawabi a ziyarar da yakai Kaduna ya na da tabin hankali.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda a Kaduna, Mansir Hassan ya fitar, ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa an haifi Muhammad da ciwon matsalar kwakwalwa.
Yan sandan sunce an bar matashin ne ya shiga wajen taron saboda an gano masoyin jam’iyar APC ne ,Kuma yana dauke da hoton Bola Tinubu da gwamna Uba Sani.
TST Hausa ta rawaito cewa tunkarar da matashin yayiwa Shugaban kasa,sai shugaban yace a kyaleshi ,amma jami’an tsaro suka kama shi.
Rahotanni sun ce mutumin ya kusanci Shugaba Tinubu yayinda yake jawabi, lamarin da ya sa shugaban ya dakata na ɗan lokaci cikin mamaki.
Jami’an tsaro na shugaban kasa sun hanzarta dakile aniyar mutumin kafin ya kusanci shugaban, tare da kama shi.
Daga bisani, shugaban ya cigaba da jawabin ba tare da wani cikas ba duk da abin da ya faru wanda ya ɗan tayar da hankali.
Shugaban ya kai ziyara Jihar Kaduna domin kaddamar da ayyukan da Gwamna Uba Sani ya aiwatar lokacin da lamarin ya faru.

