Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada aron majalisar zartaswarsa ga kananan yara yan Furamare a wani mataki na girmama bangaren Ilimi a jihar Kano.
Yaran yan makarantar Furamare a kano sun zauna zaman majalisar zartaswar na Kano na Aro ne a yayinda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yake kaddamar da rabon kayan makaranta ga daliban Furamare aji na daya a kananan hukumomi 44
Dalibai 789,000 a makarantun Furamare 7,092 zasu amfana da kayan makarantar kyauta.
Zaman majalisar na aro Wanda ya hada da Gwamnan kano daga cikin kananan yaran da Mataimakin gwamna da sauran kwamishinoni ,na Aro da aka samar sun bayyana yadda gwamna Yusuf yake zaman majalisar zartaswar Kuma sunfi magana akan ciyar da ilimi gaba.
Gwamna Yusuf ya yabawa yaran tare da jaddada mahimmacin ciyar da Ilimi gaba.