Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ketare
  • Siyasa
  • Noma da Kiwo
  • Yanayi
  • Tsaro
  • Karin Wasu
    • Kasuwanci
    • Ilimi
    • Nishadi
    • Muhalli
    • Lafiya
    • Ra’ayi
    • Wasanni
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp Telegram
TST HAUSATST HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    Yanzu Yanzu :Saudiyya Ta Takaita Wa’adin Amfani da Bizar Umarah Zuwa Kwanaki 30 Maimakon Wata 3

    March 1, 2026

    Gwamnatin Kano ta kwato motocin Tsaffin kwamishinonin da suka bi tsarin Kwankwaso

    February 26, 2026

    Hajj 2026: Hukumar Alhazan Kano ta sanar da ranar fara Jigilan Maniyata zuwa Saudiyya

    February 25, 2026

    Zaɓen Cike Gurbi a Kano Ya Tabbatar da Sauyin Salo a Siyasar Jihar – Gwamna Yusuf

    February 21, 2026

    Gwamnatin Kano ta kaddamar da motocin zagayen duba yadda ciyar da abincin Ramadan ke tafiya

    February 21, 2026
  • Ketare

    Yau Ake Toshe Shafukan Sada Zumunta na Yara yan Kasa da Shekara 16 a Australia

    December 4, 2025

    Rikicin Gaza:Sarkin Saudiyya ya amincewa Falasdinawa 1000 su shiga kasar su sauke farali kyauta

    May 19, 2025

    Duk wanda ya yarda zai bar Amurika ya koma kasarsa zamu bashi kyautar Dala 1000 – Inji Trump

    May 6, 2025

    Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya ba

    March 29, 2025

    An ga watan Sallah karama a Saudiyya

    March 29, 2025
  • Siyasa

    Majalisar Dokokin Kano ta Magantu kan Bukatar Mataimakin Gwamnan Jiha Aminu Gwarzo Ya yi Murabus

    January 31, 2026

    Shafin Kwankwasiyya Reporters a Facebook Ya Sauya Suna Zuwa Gida Gida Reporters

    January 26, 2026

    Yanzu Yanzu :Yan Majalisar Dokokin Rivers sun fara shirin Sauke Gwamnan jihar Fubara da Mataimakiyarsa daga Mulkin Jihar

    January 8, 2026

    Gwamna Yusuf Na da ‘Yancin Barin NNPP Zuwa APC kamar yadda Kwankwaso ya Bar PDP Zuwa NNPP – Shekarau

    January 6, 2026

    Dole ka daina tsoma Baki a harkokin APC, Ba zamu Bari Yadda ka Rusa PDP ka yiwa APC haka ba – Sakon Hotoro ga Wike

    January 6, 2026
  • Noma da Kiwo

    Za’a samu ƙarancin shinkafar Basmati da Indiya ke nomawa a bana

    September 4, 2025

    Tsadar rayuwa: Komai matsayin mutum a Najeriya ya koma gona,saboda abinda na hango -Inji wani Lauya

    December 15, 2024
  • Yanayi
  • Tsaro

    A Wasan Hausa na koyi yadda ake sace Mutane – In ji Matashin da DSS suka kama a Kano

    February 13, 2026

    Duk wanda ya Kashe Wani a nemi shawarar Malamai a aika shi Lahira Kawai – Sheikh Daurawa

    January 18, 2026

    An sako Yan Mauludi 28 da aka sace tun 2025 a Filato

    January 10, 2026

    An Sace Amarya da Kawayenta 14 a Sokoto ana Tsaka da Shagalin Biki Yau Lahadi

    November 30, 2025

    RASHIN TSARO: Gwamnonin Katsina da Plateau sun rufe makarantun jihar nan take

    November 21, 2025
  • Karin Wasu
    1. Kasuwanci
    2. Ilimi
    3. Nishadi
    4. Muhalli
    5. Lafiya
    6. Ra’ayi
    7. Wasanni
    8. View All

    Yan Najeriya basa shayin kashe Kudi, sunyi amfani da Fetur na Naira Tiriliyan 1.58 a Bikin Kirsimeti -In Ji Gwamnatin Tinubu

    January 22, 2026

    Dangote ne ya rage farashin fetur da kaso 5.6%, shi ya sa farashi ya sauka ba saboda janye harajin 15% ba.

    November 19, 2025

    Dangote ya buɗe sabon kamfanin siminti mai darajar CEFA biliyan 100 a Côte d’Ivoire

    October 13, 2025

    Dangote ya ƙaddamar da gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 2.5 a Habasha

    October 4, 2025

    Ayyukan Cigaban Ilimi a Kano Sun Wuce Zato, Gwamna Yusuf Ya Sauya Alkibla – Kwamared Waiya

    February 25, 2026

    Marubuciyar Najeriya, Dr Asma’u Isah Maibasira, Ta Kaddamar da Littafin Jagoranci a Birtaniya

    February 7, 2026

    An yi taron Murnar cika shekaru 30 da samar da Cibiyar addini ta Usman bn Affan Gadon Kaya wacce Marigayi Sheikh Ja’afar ya Kafa

    February 1, 2026

    Wasika zuwa ga Gwamnan Kano kan bukatar Samar da Tsaro a makarantu ko Rufe su – Tsohon Kwamishinan Ilimi Sunusi Kiru

    November 24, 2025

    An Amince da Fara Shirya Fim ɗin Maitatsine – Darakta

    January 9, 2026

    Karamin Yaron da Kakarsa Ta yi Sanadiyar Daukakarsa a Duniya ya Cika Shekara 12

    December 14, 2025

    MUTU KA RABA — HISBA ta ce aure tsakanin Mai Wushirya da ‘Yar Guda ba ta dauke shi da wasa ba

    October 21, 2025

    Majalisar Yara: Gwamna Yusuf ya baiwa yara aron zaman majalisar zartaswarsa a Kano dan girmama Ilimi

    January 13, 2025

    Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar cin tarar kuɗi ga duk wanda ya sake tofar da yawu ko majina akan hanya

    February 3, 2025

    Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta dauki sabbin matakan kare Muhalli

    January 31, 2025

    Daga yanzu an daina barin tilin shara akan titunan birnin Kano – Gwamnatin Kano

    January 13, 2025

    Da ’Yan Najeriya Sun San Haɗarin Abincin da Ake Shanyawa a Gefen Hanya, Ko Kyauta Aka Ba Su Ba Za Su Ci Ba — Masana

    January 30, 2026

    WHO Ta Yi Kira Da A Kara Haraji Kan Barasa Da Abubuwan Sha Masu Dauke Da Sikari

    January 14, 2026

    Tinubu Naira 10,400 kacal ya warewa kowane ɗan Najeriya a fannin lafiyarsa cikin kasafin kuɗin 2026 – NMA

    December 29, 2025

    Gwamna Yusuf ya amince da Kashe kuɗi naira miliyan 164 domin sake gyara Asibitin Asiya Bayero

    November 2, 2025

    Ya kamata Hisba da Malamai a Kano su bayyana matsayinsu kan yadda yan siyasa ke jifan juna da kalmar LUWADI – Anas Hassan

    February 24, 2025

    Labarin dan Jaridar da ya kafa tarihi a duniyar yada labarai a kafar sadarwa ta zamani

    February 3, 2025

    Burinmu a yanzu shine Barau FC ta samu gurbin shiga gasar zakarun Nahiyar Africa – DSP Barau

    February 25, 2025

    An karrama jagoran kwallon kafa na Barau Jibiril Academy da lambar gwarzon shekara a bangaren Shugabanci

    December 21, 2024

    Yanzu Yanzu :Saudiyya Ta Takaita Wa’adin Amfani da Bizar Umarah Zuwa Kwanaki 30 Maimakon Wata 3

    March 1, 2026

    Gwamnatin Kano ta kwato motocin Tsaffin kwamishinonin da suka bi tsarin Kwankwaso

    February 26, 2026

    Hajj 2026: Hukumar Alhazan Kano ta sanar da ranar fara Jigilan Maniyata zuwa Saudiyya

    February 25, 2026

    Ayyukan Cigaban Ilimi a Kano Sun Wuce Zato, Gwamna Yusuf Ya Sauya Alkibla – Kwamared Waiya

    February 25, 2026
TST HAUSATST HAUSA
Home » Labarin dan Jaridar da ya kafa tarihi a duniyar yada labarai a kafar sadarwa ta zamani
Ra'ayi

Labarin dan Jaridar da ya kafa tarihi a duniyar yada labarai a kafar sadarwa ta zamani

By tstFebruary 3, 20256 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
FB IMG 1738577671037

Daga Malam Anas Idiris Hassan

Sannu a hankali bayan da duniyar yada labarai a sassa daban daban ke kara samun sauyi ciki harda Najeriya, kafafen sada zumunta na zamani na daga cikin wadanda suka fara sauya duniyar yada labarai a kowacce kasa.

Saidai a wasu lokata da dama masu amfani da kafar sada zumunta din sunfi maida hankali wajen yada labaran karya,da labaran da zasu haifar da rigima da sauransu wanda anfi zargin cewa yawanci wadanda basu da gogewa a aikin jarida sune sukafi maida hankali a irin wannan bangaren.

Kasashe irinsu Amurika da Indiya da Chaina da Rasha sune kan gaba wajen yada labaran karya a kafafen sadarwa na zamani musamman a lokutan zaben Kasashen,ta cikin wani rahoto da aka fitar a shekarar 2024.

Saidai akwai kasashen da suka tashi tsaye haikan wajen yaki da labaran karya,Kuma sukayi nasara kamar ,Kasar Barazil da Finland da Maxico da Norway da sauransu.

TST Hausa ta rawaito cewa duk da Najeriya bata cikin manyan kasashen duniya da suke fama da yada labaran karya a kafafen sadarwa  na zamani amma kasar ta fuskanci kalubale mai yawa na yada labaran karya,musamman a duk lokutan zabe,Inda koda a zaben 2023 da ya wuce an yada labaran karya mai yawa da yake da alaka da zaben.

Misalin labaran karya da aka yada a game da zaben 2023 shine yadda wani dalibi mai shekara 23 dan asalin jihar Lagos ya yada labaran karya akan Peter Obi na jami’yar Labor party wanda yake neman takarar Shugabancin Najeriya,inda matashin ya wallafa cewa Peter Obi ya rabawa mabiya addinin kirista kudi a coci domin a zabeshi.

Sannan matashin ya yada cewa dan takarar Shugabancin Najeriya a jami’yar NNPP sanata Rabiu Musa kwankwaso bashi da digirin digir gir na karatu daga jami’a.

Daga baya duka yan siyasar  suka karyata labarin.

Kafin nan a shekarar 2019 lokacin da Buhari yake neman wa’adi na biyu an yada cewa ya mutu a Asibtin da yake zuwa jiya a Burtaniya daga baya fadar Shugaban kasa ta musanta labarin.

A Najeriya din dai,anyi amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen yada labaran karya game da cutar Coronavirus ,cutar da ta billa a China daga baya ta bazu sassan duniya.

Har yanzu Najeriya na fama da labaran karya a kafar sadarwa ta zamani musamman abinda ya shafi siyasa da tattalin arziki da koshin lafiya da zamantakewar jama’a.

Kuma duka wannan na fitowa ne daga kafar sadarwa ta zamani ga masu anfani da ita wadanda ake zargin basa  samun  horo na musamman.

Saidai da alama zuwan kungiyoyin masu yada labarai a kafar sadarwa ta zamani ya iya kawo  sauyi a Najeriya.

Anan Arewancin Najeriya Kungiyar masu yada labarai a kafar sadarwa ta zamani wato Online Media ta zabi Kwamared Musa Muhammad daga jihar Kaduna a matsayin sabon shugabanta na kasa shiryar  Arewa.

Muhammad ya samu kuri’u 287 inda ya kayar da abokin takararsa, kwamared Lynn Adda, tsohon shugaban Kungiyar yan jarida NUJ na jihar Taraba, wanda ya samu kuri’u 138.

Kwamared Femi Adi daga jihar Kogi shine ya zama babban sakataren Kungiyar da kuri’u 210 Inda ya kayar da kwamared Rayyan Al-Hassan, wanda ya samu kuri’u 207.

A jawabinsa na karabar ragamar Shugabancin Kungiyar na Arewa Kwamared Musa Mohammed ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da ke jihohin Arewa 19 da su yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yakar labaran karya da inganta shugabanci na gari.

A cewarsa, dandalin sada zumunta na yanar gizo na iya zama abin dogaro ne kawai don yada labarai lokacin da kwararrun ‘yan jarida suka karbe ragamar aiki tare da amfani dashi ta hanyar kwarewa.

Daga nan Kano kuma,babu hamayya ,saboda kwarewarsa da gogewarsa, Kungiyar ta zabi kwamared Abbas Yushe’u Yusuf  a matsayin Ma’ajin kudi.

Abbas Yusuf ya kawo sauyi da dama bangaren yada Labarai a kafar sadarwa, Musamman kokarin fito da abu yadda yake da kuma  sanar da gwamnati ko masu ruwa da tsaki abinda ke faruwa ba tare da jin tsoro ko shayi ba.

Babban cigaban da aka samu a kano shine zaburar da matasan yan jarida kan su kafa Jaridar yada labarai a kafar sadarwa, bayan kafuwar Jaridar Nigeria Tracker a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2020 Kuma kusan itace kafar sadarwa ta biyu da tayi tashe wajen yada labarai mai inganci, Jaridar da Abbas Yusuf ya kafa bayan ya bar aiki da Freedom Radio a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2020.

An haifi Ma’ajin kuɗi na Kungiyar masu yada yada labarai a kafar sadarwa ta zamani Abbas Yusuf a watan Augusta a  shekarar 1983 a garin Dan Madanho cikin karamar hukumar Gezawa.

Abbas,ya kammala karatunsa na nazarin aikin jarida (Digirin Farko)a jami’ar Bayaro dake Kano a shekarar 2008 sanan ya koma yayi digiri na biyu wato masters a bangaren na aikin jarida a shekarar 2017 a jami’ar ta Bayaro.

A halarci taron karawa juna sani akan aikin jarida a wurare daban daban a fadin Najeriya,sannan daga shekarar 2017 zuwa 2019 ya halarci taron karawa juna sani a jami’ar Northwest dake Kano kan fassara labarai.

Kafin nan Abbas Yusuf ya zamo daya daga cikin masu tace labarai a gidan Radio Freedom a shekarar 2017 zuwa 2020 bayan ya dawo daga gidan gwamnatin jihar Kano a matsayin wakilin gidan Freedom acan.

A watan Oktoban shekarar 2017 ne aka dawo da Abbas Yusuf daga gidan Freedom Radio bayan wani labari da ake zargin ya yada wanda baiyiwa gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje dadi ba ,wato kan harin da yace an kaiwa tawagarsa a hanyar Abuja, lokaci da takun saka ya fara zafi tsakanin bangaren Ganduje da Sanata Kwankwaso.

Sabon Ma’ajin kuɗi na Kungiyar masu yada labarai a kafar sadarwa ta zamani,ta Arewa Abbas Yusuf duka kafin nan shine dan jarida na farko da ya wakilci Rahma Radio farin cikin al’umma a gidan gwamnatin Kano a shakerar 2011 zuwa 2012 kafin ya koma Freedom Radio,kuma suka amince yaci gaba da zama a gidan gwamnatin daga shekarar 2012 zuwa 2017.

Bayan ya ajiye aikin yada labarai a Radio a shekarar 2020 ,Abbas Yusuf ya kafa gidan jarida na Nigeria Tracker Wanda shine Shugabanta.

A dalilin haka ne ya taba rike kujerar babban Sakataren Kungiyar masu yada labarai a kafar sadarwa ta zamani (Online Media) na kasa reshen Kano daga nan kuma a yanzu yake rike da Ma’ajin kuɗi na Kungiyar reshen Arewa mai jihohi 19 a sabon zaben da akayi a Kaduna.

Bayan kafa Jaridar Nigeria Tracker, Abbas Yusuf ya taimakawa marasa karfi da masu bukata ta musamman da gano wasu kura kurai da yan siyasa keyi a cikin gwamnati a Kano dama Najeriya da nufin gyara ko gano bakin zaren.

Har yanzu kuma ba’a sani ba ko Abbas Yusuf ya na da sha’awar shiga siyasa anan gaba.

Saidai a shekarar 2023 ya rike Daraktan yada labarai na kwamatin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Kano a jami’yar ADP Sha’aban Ibrahim Sharada.

Share. Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp

Related Posts

Ya kamata Hisba da Malamai a Kano su bayyana matsayinsu kan yadda yan siyasa ke jifan juna da kalmar LUWADI – Anas Hassan

February 24, 2025
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Yanzu Yanzu :Saudiyya Ta Takaita Wa’adin Amfani da Bizar Umarah Zuwa Kwanaki 30 Maimakon Wata 3

March 1, 2026

Gwamnatin Kano ta kwato motocin Tsaffin kwamishinonin da suka bi tsarin Kwankwaso

February 26, 2026

Hajj 2026: Hukumar Alhazan Kano ta sanar da ranar fara Jigilan Maniyata zuwa Saudiyya

February 25, 2026

Ayyukan Cigaban Ilimi a Kano Sun Wuce Zato, Gwamna Yusuf Ya Sauya Alkibla – Kwamared Waiya

February 25, 2026

Zaɓen Cike Gurbi a Kano Ya Tabbatar da Sauyin Salo a Siyasar Jihar – Gwamna Yusuf

February 21, 2026
Advertisement
© 2026 TST HAUSA Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.