Jami’an tsaro sun kama shahararren mawakin siyasa dake yiwa Sanata Kawu Sumaila da Alassan Ado Doguwa waka wato Malam Idris Dan Zaki Burum – Burum.
Rahotanni nacewa har Yanzu ba, a bayyana dalilan da suka sa aka kama wakin ba .
Saidai wata majiya daga garin Burum-Burum nacewa ,watakila kama mawakin na da nasaba da zargin cin fuska da sakin harshensa da yayi akan jagoran kwankwansiyya Sanata Dr Rabiu Musa kwankwaso da gwamnatin Kano.
Wasu daga cikin kalaman batancin da ake zargin mawakin na Alassan Doguwa da Kawu Sumaila wato Dan Zaki yayi ,sun hada da “Kwankwansiyya kabarin bature ,da Kuma rera wakar Allah ya isa tsakaninsa da gwamnatin kano ,An zuba yan tamore a gwamnati ,in banda mugun hali ka zuba wasu a daki ,ga tarin marasa amfani ,da Kuma sauran baituka na zage zage a cikin wakar ,da shagube “Kamar yadda TST Hausa ta samu Kofin kadan daga cikin wakar”