Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya miƙa saƙon taya murna ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa cikarsa shekaru 63 a duniya.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2026 ne Gwamna Yusuf ke cika shekara 63 da haihuwa.
Shugaban Ƙasar ya yaba da gaskiya,da kamun kai, da tawali’u da jajircewar gwamna Abba Kabir Yusuf wajen hidimar al’umma, yana mai cewa waɗannan siffofi sun bayyana a yadda yake tafiyar da mulki a Jihar Kano.
Sanarwar tace an zaɓi gwamna Yusuf a shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamnatin-kano-ta-haramta-samar-da-hisba-mai-zamanta-kanta-a-jihar/
A baya, ya riƙe muƙamin Kwamishinan Ayyuka,da Gidaje da Sufuri daga 2011 zuwa 2015, a lokacin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa mulkin gwamna Yusuf a Kano wadda ke ɗaya daga cikin ginshiƙan siyasa cigaba a Arewa na nuna jajircewa wajen bunƙasa cigaban al’umma, musamman a matakin ƙasa da rage raɗaɗin talakawa, bisa tafarkin akidar marigayi Mallam Aminu Kano.
A cewarsa:
“Ƙwarewar shugabanci da Gwamna Yusuf ya samu a matsayinsa na kwamishina, inda ya kula da muhimman ma’aikatu, ta taimaka wajen shirya shi don sauye-sauyen gine-gine da ake gani a Kano a yau.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-ya-yabawa-gidauniyoyi-biyu-kan-gudun-mawar-mota-da-suka-bayar-domin-jin-kai/
Ya kaddamar da shirye-shiryen sabunta birane, gina gadoji da hanyoyin mota, ciki har da titunan kilomita biyar a kowace ƙaramar hukuma.
Haka kuma,Tinubu yace bayyana dokar ta-baci a fannin ilimi da Gwmana Yusuf ya yi ya haifar da ingantaccen ci gaba a sakamakon jarabawar NECO da daliban Kano ke samu.
Shugaban Ƙasa ya yi wa Gwamnan Kano fatan tsawon rai, lafiya da ƙarin damar ci gaba da jagoranci mai kawo sauyi a jihar.

