Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar jihar murnar zagayowar ranar Eid-el-Fitr, wadda ke nuna kammala azumin watan Ramadan mai albarka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamna Yusuf ya bayyana Sallah karama a matsayin lokaci na godiya ga Allah, tunani mai zurfi, da kuma sabunta kuduri kan kyawawan dabi’u na addini, hadin kai da jin kai, kamar yadda aka nuna a tsawon watan Ramadan.
Ya bukaci al’ummar jihar da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da tsari, tare da gargadin su da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin ci gaba da wanzar da zaman lafiya, hakuri da juna, da mutunta juna a tsakanin al’umma, ba tare da la’akari da bambance-bambance ba.
Haka kuma, ya bukaci iyaye da masu kula da yara da su ja hankalin ‘ya’yansu da wadanda ke karkashinsu su zama masu bin doka da oda, tare da nuna halaye nagari a lokacin bukukuwan Sallah.
Gwamna Yusuf ya kuma karfafa gwiwar al’umma da su nuna soyayya tare da taimakawa marasa galihu, daidai da koyarwar addinin Musulunci.
Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da cewa an dauki dukkan matakan tsaro da suka dace domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali a fadin jihar Kano.
A karshe, Gwamnan ya yi wa daukacin al’ummar Kano fatan alheri, tare da yi musu fatan Sallah mai dadi, lafiya da albarka.

