Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada ƙudurin ta na ƙara inganta aiki tare da ɗaga darajar Hukumar Zaɓe ta Jihar mai zaman kanta (SEC), domin tabbatar da sahihanci, gaskiya da adalci a dukkan zaɓukan ƙananan hukumomi.
Gwamnan jihar, Umar Namadi, ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar da Alhaji Rabiu Yarima a matsayin sabon kwamishinan hukumar zaɓen jihar.
A cewarsa, ingantacciyar hukuma mai zaman kanta ita ce ginshiƙin dimokuraɗiyya, don haka gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa wa hukumar domin ta gudanar da aikinta cikin ƙwarewa da gaskiya.
Gwamnan ya bayyana Rabiu Yarima a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati mai tarin ƙwarewa, wanda ya shafe shekaru da dama yana hidimtawa jihar a fannoni daban-daban. Ya kuma buƙace shi da ya yi amfani da wannan ƙwarewa wajen kawo sauyi mai ma’ana da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumar zaɓen.
A nasa jawabin, sabon kwamishinan hukumar zaɓen, Alhaji Rabiu Yarima, ya nuna godiya ga gwamnan bisa amincewar da aka nuna masa, tare da alƙawarin gudanar da aikinsa bisa gaskiya, rikon amana da bin doka.
Ya ce zai mayar da hankali wajen sabunta tsarin aiki na hukumar, da inganta sahihancin zaɓe, tare da tabbatar da adalci ga dukkan ‘yan siyasa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko matsayi ba.
Haka kuma, ya jaddada aniyarsa ta yin aiki kafada da kafada da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an gudanar da zaɓuka cikin lumana da karɓuwa ga kowa.
Alhaji Rabiu Yarima dai tsohon babban sakatare ne a aikin gwamnati, inda ya yi aiki a ma’aikatu daban-daban kafin ya yi ritaya. Haka zalika, ya taɓa riƙe muƙamin Babban Mataimaki na Musamman ga gwamnan jihar, abin da ke ƙara nuna ƙwarewarsa a harkokin mulki da shugabanci.
Bikin rantsuwar ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar, kwamishinoni, da sauran manyan jami’an gwamnati, inda aka bayyana faton cewa sabon kwamishinan zai taka rawar gani wajen inganta tsarin zaɓe a jihar.

