Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya mika sabbin motoci 10 masu amfani da CNG ga kungiyar kwadago ta Najeriya reshen Kano.
A yayinda yake jawabi a wajen kaddamar da motocin ,gwamna Abba ya ce samar da motocin zai saukakawa ma’aikata musamman a wannan lokaci da ake rayuwa babu tallafin man fetur.
Gwamna Abba Kabir ya kuma yi alkawarin gina sabuwar cibiyar horos da ma’aikata a harabar kungiyar gwadago ta Kano, inda a nan ne aka kaddamar da motocin na CNG
Gwamna Abba ya ce motocin da shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo Kano zasu taimaki ma’aikata da sauran al’umma bama Kano kadai ba harda sauran jihohin Najeriya.
Anasa jawabin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC Comrade Joe Ajaero ya yabawa gwamnatin Kano abisa samar da walwalar ma’aikata da akeyi .
Haka shima mataimakin shugaban NLC na kasa kuma shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya na Najeriya Kwamred Kabiru Ado Minjibir Magayakin Minjibir yace kokari da gwamantin kano tayi daga cikin abinsa kungiyar ke bukata
Kwamred Ado Minjibir ya kuma jinjinawa gwamntin ta Kano abisa fara aiwatar da dokar mafi karancin albashin ma’aikata.

