Shugaban Jam’iyyar APC na ƙsaa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana Gwamna Sim Fubara a matsayin jagoran jam’iyyar a Jihar Ribas.
Yilwatda ya kuma ce zai mara wa Fubara baya a wa’adi na biyu idan ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Da yake magana a wani shiri na musamman a gidan Talabijin din Channels Yilwatda ya ce gwamna Fubara shi ne jagoran APC a Ribas, amma dole ne ya yi aiki tare da sauran shugabannin jam’iyyar a jihar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-da-apc-sun-yiwa-gwamnan-kano-yusuf-maraba-cikin-apc-sun-shirya-karbarsa-hannu-biyu-abdullahi-abbas/
Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sake tashin rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan matsayin jagoranci a jihar.
A watan Disamba da ya gabata, bayan sauya shekarsa zuwa APC, Fubara ya ayyana kansa a matsayin jagoran jam’iyyar a Ribas, bayan da aka ba shi katin zama ɗan jam’iyya mai lamba 001.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-ya-nada-sabon-gwamnan-jihar-rivers-na-rikon-kwarya/
Sai dai Wike ya yi watsi da wannan iƙirarin, inda ya ce shi ne ke da ikon sarrafa tsarin siyasa a jihar, ganin cewa APC da PDP sun haɗa kai wajen mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen 2027.

